Tinubu Ya Yi Martani kai Tsaye ga Masu Cewa Ya Tsorata game da 2027

Tinubu Ya Yi Martani kai Tsaye ga Masu Cewa Ya Tsorata game da 2027

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan cewa yana jin tsoron zaben 2027 saboda yadda 'yan adawa suka yunkuro da karfi a ADC
  • Ya yi martani ne yayin tattaunawa da jakadun da ke yada manufofin shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026
  • Tinubu ya yi magana kan girmama umarnin kotu, musamman lura da cewa jam'iyyar ADC ta gudanar da babban taron ta na kasa duk da tana cikin shari'a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya fito da kan shi yana kore jingina masa tsoro da wasu ke yi game da zaben 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da zabe ke kara karatowa kuma 'yan adawa ke nanata cewa za su fatattake shi daga fadar shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 da suka sa ake ganin shugaban INEC ba zai yi adalci ba a 2027

Shugaba Bola Tinubu na jawabi a fadar shugaban kasa.
Lokacin da Bola Tinubu ke karyata cewa ya tsorata kan zaben 2027 a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Tinubu ya yi ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na X bayan tattaunawa da wasu 'yan APC a fadar shugaban kasa.

Da gaske Bola Tinubu ya tsorata?

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai ji tsoron wadanda ke shirin cewa za su kwace mulkin Najeriya daga hannun shi a zaben shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da mambobin kungiyar Renewed Hope Ambassadors karkashin jagorancin gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma.

Shugaban ya ce yana da kudurin amfani da damar da ya samu domin yaki da talauci da jahilci a kasar, tare da dasa ‘yanci a zukatan ‘yan Najeriya da kuma tabbatar da dorewar dimokuradiyya.

Yayin da yake sukar ‘yan adawa, ya ce gwamnatinsa ba za ta saba wa umarnin kotu ba, yana mai cewa dole ne a mutunta bangaren shari’a, ko da kuwa hukuncin ya yi musu dadi ko akasin haka.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta firgita da kalaman Atiku kan 2027, ta yi masa martani

Daily Trust ta rahoto ya ce:

“Kuna son ku tsorata ni ne? Ba zai yiwu ba. Na taba bin wannan hanya (ta adawa) a baya,”

In ji shi.

Bola Tinubu da 'yan APC a fadar shugaban kasa
A lokacin da Bola Tinubu ke bayani ga 'yan APC a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya soki 'yan adawa

Shugaban ya kara da cewa wadanda ke kokarin karbe mulki a hannun shi a 2027 suna da tarihin gazawa, yana mai cewa hakan na nuna rashin kwarewarsu.

“Babu wanda ba mu san tarihinsa ba a cikinsu. Wani daga cikinsu ya taba zama shugaban majalisar kasa kan harkokin sayar da kadarorin gwamnati (NCP), sun sayar da kamfanin karafa na Delta State, yana aiki yanzu? A’a.
"Sun sayar da kamfanin Ajaokuta, yana aiki yanzu? A’a."

Shugaba Tinubu ya bayyana zaben fidda gwani da ya kai shi kan mulki a matsayin mai wahala, yana mai cewa zaben gama gari ma ya kasance mai tsauri, amma ya shawo kan dukkan kalubalen.

Ga bidiyon da Bola Tinubu ya yi bayani a kasa:

Hadimin Tinubu ya soki Atiku

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

A wani labarin, mun kawo muku cewa Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya caccaki Atiku Abubakar kan cewa zai yi takara a 2027.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa Atiku na so rusa tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa, inda ya ce wajibi ne shugaba Bola Tinubu ya yi shekara takwas.

Atiku Abubakar na cikin manyan 'yan adawa da suka sha alwashin kifar da Tinubu a zabe mai zuwa, kuma ya ce ba zai sake takara ba bayan 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng