Gwamnatin Amurka zata baiwa Najeriya tallafin $2.1 billion na cigaba

Gwamnatin Amurka zata baiwa Najeriya tallafin $2.1 billion na cigaba

  • Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana niyyar taimakawa Najeriya wajen kawar da matsalar tsaro
  • A wani sabon kudin tallafi da tayi alkawari, tana son ayi amfani da su wajen inganta ilmi da kiwon lafiya
  • Amurka tayi alkawari turo adadi mai yawa na rigakafin kawo karshen shekara, kyauta kuma babu ko sisi

Gwamnatin Amurka ta rattafa hannu kan takardan yarjejeniyar tallafin $2.1 billion ga Najeriya domin taimaka mata wajen farfadowa daga annobar COVID-19 da kuma tattalin arziki.

Wannan ya faru ne lokacin da Sakataren wajen Amurka, Antony Blinken ya kawo ziyarar aiki Najeriya, rahoton PremiumTimes.

A hira da manema labarai, Blinken yace wannan tallafi zai taimakawa Najeriya wajen cigaba a bangarorin daban-daban.

A jawabin da yayi, yace wannan "babban zuba jari ne wajen inganta ilimi, kiwon lafiya, da wasu ayyukan jin dadi da yan Najeriya ke nema domin nasara a nan gida da kuma waje."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga

Sakataren wajen Amurka
Gwamnatin Amurka zata baiwa Najeriya tallafin $2.1 billion na cigaba Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Muna hada kai wajen kawar da Boko Haram da ISWAP

Blinken ya kara da cewa Amurka na hada kai da Najeriya wajen magance matsalar tsaro, wanda ya hada da Boko Haram, ISWAP da yan bindiga.

A cewarsa:

"A ganawata da shugaban kasa, mataimakin Shugaban kasa, da ministan waje, mun tattauna muhimmancin samar da hanya mai kyau wajen magance matsalar tsattsaurin ra'ayi da kuma kare hakkin dan Adam a Najeriya."
"Lamarin Najeriya na shafanmu kulli yaumin a Amurka, saboda karfinta a waje."

Mun baku rigakafi gudan milyan 7.6

Blinken ya cigaba da cewa Najeriya ta samin kwayar rigakafin Korina guda milyan 7.6 daga Amurka.

Yace:

"Mun sa ran sake turo adadi mai yawa na rigakafin kawo karshen shekara, kyauta kuma babu ko sisi."

Kara karanta wannan

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel