Naja'atu: Yadda Ƴan Najeriya za Su Yi Amfani da ADC a Kifar da APC a 2027

Naja'atu: Yadda Ƴan Najeriya za Su Yi Amfani da ADC a Kifar da APC a 2027

  • Fitacciyar ƴar siyasa a Najeriya, Hajiya Najaatu Muhammad ta ce ADC ce injin ceto Najeriya daga bakin da ta ke ciki a 2027
  • A yayin da ta ke jawabi a wajen babban taron jam'iyya da ya gudana a Abuja, ta ce zaɓe mai zuwa ba wai tsakanin ADC da APC ba ne
  • Ta bukaci ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen mulkin rashin adalci da ta ce ana yi masu a ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu da APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Fitacciyar ‘yar siyasa kuma mai fafutukar kare hakkin jama’a, Naja’atu Muhammad, ta bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su tashi tsaye domin kwato kasarsu daga abin da ta kira mulkin danniya.

Kara karanta wannan

Duk da Kwankwasiyya ta bar NNPP, jam'iyyar na ci gaba da kuka da INEC

Ta yi wannan jawabi ne a wajen taron kasa na jam’iyyar ADC da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026.

Naja'atu ta ce ADC ca za ta zama gatan Najeriya
Hajiya Naja'atu Muhammad a wurin taron ADC da ya gudana a Abuja Hoto: Rariya
Source: Facebook

A cikin bidiyon jawabinta da Premium Times ta wallafa, Hajiya Naja'atu Muhammad ta jaddada cewa jam’iyyar na da muhimmiyar rawa wajen ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Muhimmancin ADC wajen kifar da APC

A bidiyon da Alhaji Salisu Adamu ya wallafa a Facebook, Naja'atu Muhammad ta bayyana ADC a matsayin “injin” da ‘yan Najeriya za su yi amfani da shi wajen kubutar da kasar daga matsalolin da suka dabaibaye ta.

Ta ce:

"A yau muna cewa ADC ita ce injin da ‘yan Najeriya za su yi amfani da shi wajen ceto Najeriya. Ba mu da wani zabi.”

Ta kara da cewa bai kamata a dauki batun a matsayin takara tsakanin jam’iyyu biyu ba, inda ta ce yanzu haka matsalar ta fi ƙarfin haka.

Naja'atu Muhammad ta ce ƴan Najeriya sun gaji da APC
Tsohon gwamna Rotimi, Hajiya Naja'atu Muhammad da David Mark a babban taronsu na ADC a Abuja Hoto: ADC Kwankwasiyya
Source: Facebook

Ta bayyana cewa:

“Idan ka ce ADC da APC ne, ka rage girman matsalar. Wannan ba batun jam’iyyu ba ne. Wannan ‘yan Najeriya ne gaba daya a cikin ADC.”

Kara karanta wannan

"Tinubu na yi wa dimokuradiyya shakar mutuwa": Obi ya ce da matsala gabanin 2027

Naja'atu ta zaburar da ƴan Najeriya a kan APC

Hajiya Naja'atu Muhammad ta bayyana cewa a ganinta, fafatawar da ke gaban kasa ita ce tsakanin talakawan Najeriya da wasu da ta kira “mafiasu” wato masu mulkin danniya da rashin tausayi.

Ta ce wadannan mutane ba su da tausayi, ba su da ka’ida, ba su da jin kai, don haka dole ne ‘yan kasa su hada kai domin tunkarar su a babban zaɓe mai zuwa.

Ta kuma bukaci duk wanda ke son ganin canji ya shiga tafiyar ADC, tana mai gargadin cewa lokaci ya kure.

A cewar ta:

“Idan kana son rayuwa gobe, dole ne ka shiga wannan jirgi. Za mu yi amfani da duk abin da muke da shi wajen rusa wannan mummunan shugabanci."

Naja'atu Muhammad ta jaddada cewa babu wata kasa da ‘yan Najeriya za su koma face Najeriya, don haka dole ne su tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancinsu.

Tsagin ADC ya dakatar da Atiku

Kara karanta wannan

SERAP ta nemi majalisa ta bi diddigi, ta binciki alaƙar shugaban INEC da APC

A baya, kun ji cewa wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ƙarƙashin Raji Zumo ya yi taron sanar da dakatar da Atiku Abubakar da wasu mutane biyu daga jam'iyyar.

Raji Zumo ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassan bogi a jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da yin watsi da umarnin kotu.

Sai dai Babachir Lawal, wanda shi ma aka dakatar da shi, ya bayyana kwamitin Raji a matsayin "masu shan wiwi" wadanda ƙwaya ta bugar kafin su yanke hukuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng