Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta

Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta

- Kasar Amurka ta nuna kwadayinta ga taimakawa Najeriya wajen yakar masu tada kayar baya

- Kasar ta bayyana cewa, ta jima da fara nuna soyuwarta ga tallafawa Najeriya harkar tsaro

- Wani jami'in kasar ya tabbatar da goyon bayan kasar Amurka ga sauyin hafsoshin tsaro

Kasar Amurka ta bayyana shirinta na taimakawa Najeriya ta kawo karshen yawan sace-sacen yara ‘yan makaranta da ake yi a sassan arewacin kasar.

Michael Gonzales, mataimakin sakatare a Ofishin Amurka na Harkokin Afirka, ya ce Amurka a shirye take tsaf ta taimaka wajen kawo karshen kalubalen tsaro idan Najeriya ta nemi taimakonta.

Ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis a yayin ganawa da manema labarai da ofishin suka shirya, wanda jaridar TheCable ta shaida.

A shekarar 2021, an sha samun kararrakin sace yara 'yan makaranta da yawa a arewacin Najeriya yayin hare-haren 'yan bindiga.

KU KARANTA: Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi

Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta
Kasar Amurka: Mun shirya tsaf domin taimakawa Najeriya kan sace 'yan makaranta Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

An gano cewa an yi garkuwa da yara sama da 1,000 daga makarantunsu a irin wadannan hare-hare a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

A jawabin da ya gabatar kan kokarin da Amurka ke yi na yaki da ta'addanci a Afirka, Gonzales ya ce Amurka ta "kyamaci" salon satar mutane da yawa wanda ya ce barazanar tsaro ce ta cikin gida.

"Mun kyamaci wannan yanayin na yawan sace 'yan makaranta kuma muna jajantawa ga mutanen da abin ya shafa da danginsu," in ji shi.

“Kasar Amurka a shirye take ta bayar da goyon bayan da ya dace ga gwamnatin Najeriya idan aka nemi hakan.

"Tsowon lokaci, muna neman taimakawa wajen bunkasa ayyukan jami'an tsaron Najeriya domin su dauki mataki yadda ya kamata game da barazanar cikin gida da kasar ke fuskanta. "

Jami'in na Amurka, ya kara da cewa Amurka ta "karfafa gwiwa" saboda shawarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yanke na sauya shugabannin hafsoshin tsaro a matsayin wani bangare na kokarin magance matsalar tsaron kasar.

"Muna fatan yin kawance da su don ci gaba da inganta karfin sojojin Najeriya don samun damar kare kai da kare mutanensu," in ji shi.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta yi watsi da tattaunawar shigo da sojojin haya na kasashen waje don yaki da masu tayar da kayar baya da sauran nau’ikan rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, The Nation ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd), ne ya fadi haka a ranar Alhamis yayin wani taron a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce gwamnatin ta gwammace ta yi amfani da dukkanin rundunoni don kawar da yakin.

Monguno ya bayyanawa manema labarai cewa, Najeriya na da ma’aikata da kayan aiki don cimma nasara kan wadannan kalubalen tsaro na cikin gida.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel