Donald Trump ya maka kamfanin Facebook da Twitter a kotu, ya bayyana dalili

Donald Trump ya maka kamfanin Facebook da Twitter a kotu, ya bayyana dalili

  • Tsohon shugaban kasar Amurka ya maka kamfanonin Facebook, Twtter da Google kan dakatar dashi
  • Ya bayyana hakan a matsayin take hakkinsa na fadin albarkacin bakinsa a matsayinsa na dan Amurka
  • An dakatar da Donald Trump daga shafukan sada zumuntan a watan Janairu bayan wani hairgizi a Amurka

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Laraba cewa yana shigar da kara a gaban kotu a kan Facebook, Twitter da Google, yana kara fadada ikrarinsa na 'yancin fadin albarkacin baki da manyan kamfanonin fasahar suka dakile.

An dakatar da Trump daga shafin Twitter da Facebook bayan da wasu gungun magoya bayansa suka mamaye Capitol a wani mummunan hari a ranar 6 ga watan Janairu, inda kamfanonin suka nuna damuwar cewa zai karfafa tashin hankali a kasar, CBSNEWS ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

Donald Trump ya maka kamfanin Facebook da Twitter a kotu, ya bayyana dalili
Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump | Hoto: hindustantimes.com
Asali: UGC

Trump ya bayyana cewa:

"Muna neman a kawo karshen hana ruwa gudu, a dakatar da garkame bakinmu da kuma dakatar da bakanta sunayenmu, dakatarwa da sokewa da kuka sani sarai."
"Ina da kwarin gwiwa cewa za mu cimma nasarar tarihi ga 'yancin Amurkawa kuma a lokaci guda 'yancin fadin albarkacin baki."

Donald Trump ya bayyana sunayen masu kamfanonin karara yayin sanar da shigar da karar

Ya shaidawa manema labarai kamar yadda jaridar AFP ta ruwaito cewa:

“A yau, tare da Cibiyar Nazarin Manufofin Amurka ta Farko, ina shigar da babbar kara a matsayin jagoran kan gaba, game da manyan kamfanonin fasahar da suka hada da Facebook, Google da Twitter da shugabanninsu, Mark Zuckerberg, Sundar Pichai da Jack Dorsey..."

Manyan kamfanonin fasaha na kasar amurka sun zama “masu tilastawa ba bisa bin doka da oda ba,” in ji Donald Trump, wanda aka dakatar a shafin Facebook ranar 6 ga watan Janairun bana.

KARANTA WANNAN: Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

Bayan Najeriya, An Shigar da Karar Twitter a India Kan Yunkurin Cutar da Kasar

A wani labarin daban, Wata kungiya a India ta shigar da karar shugaban ofishin Twitter da ke kasar bayan da Twitter ya wallafa taswirar kasar a shafinta.

Taswirar ta nuna duka yankunan Jammu da Kashmir, wadanda ke rikici da Pakistan da kuma Ladak da ke yankin Buda a wajen Indiya.

Wannan dai ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, amma daga baya an cire bangaren daga shafin Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel