Alkalin Kotun koli ya tabbatar da nasarar Joe Biden a Jihar Pennsylvania
-Abokin tafiyar Donald Trump ya kai kara game da zaben 2020 a gaban kotu
-Mike Kelly ya roki Kotu ta haramta amfani da kuri’un E-mail a Pennsylvania
-Alkalai sun ki yin na’am da hakan, ma'ana Donald Trump ya rasa jihar a bana
A ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020, kotun kolin kasar Amurka ta yanke hukunci a game da wata kara da Donald Trump ya shigar a kan zaben da aka yi.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana kokarin ganin an ba shi nasara kan Joe Biden a zaben bana, yunkurin da yake ta yi a gaban kuliya bai kai ga ci ba.
Alkalin kotun koli ya ki bada damar a bibiyi wadanda suka kada kuri’a a zaben shugaban kasar a jihar Pennsylvania, jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto.
KU KARANTA: Donald Trump zai nemi sake neman takara a 2024
Kotun koli wanda ita ce babbar kotu a Amurka ba tayi karin bayani game da abin da ya sa tayi fatali da karar da na-kusa-da shugaban kasar suka shigar ba.
Donald Trump ne ya nada Alkalai uku daga cikin tara da ake da su a babban kotun Amurkan.
Fiye da wata guda kenan da yin zaben shugaban kasa, amma Donald Trump ya ki amincewa shi ne ya fadi zabe – a hannun ‘dan takarar hamayya, Joe Biden.
Donald Trump ya na zargin cewa akwai murdiya a ratar kuri’a miliyan bakwai da jam’iyyar hamayya ta samu, don haka magoyansa ke ta shigar da kara.
KU KARANTA: Trump ya sallama, ya yarda ya fadi zabe
‘Dan majalisar jam’iyyar Republican, Mike Kelly, ya roki kotu ta haramta kuri’un akwatin E-mail da aka yi amfani da su a jihar Pennsylvania, amma bai dace ba.
Da wannan mataki da kotu ta dauka jiya na watsi da shari’ar Mike Kelly, Alkalan kotun koli sun nuna cewa babu ruwansu da abin da ya shafi sauraron korafin zabe.
A gida Najeriya kun ji yadda kungiyar ACYY ta matasan Arewa ta ke neman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige Hafsoshin tsaro da Ministan ayyuka.
Matasan na Arewa sun hura wuta sai an tsige Raji Babatude Fashola da duka shugabannin soji, wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tun a 2015.
ACYY ta bukaci a sallami shugabannin sojin ne saboda a samu tsaro a yankin Arewacin kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng