Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka

Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka

- Akalla yan Najeriya uku ne suka yi nasara a zaben 2020 na kasar Amurka

- An gudanar da zaben ne a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba

- Esther Agbaje, Oye Owolewa da kuma Nnamdi Chukwuocha ne yan Najeriyan da suka yi nasara a zaben

Ga jerin yan Najeriya uku da suka yi nasara a kasa, kamar yadda rahoton Premium Times ya nuna.

KU KARANTA KUMA: Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi

Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka
Jerin sunayen ƴan Nigeria guda 3 da suka lashe zaɓen kujerar majalisar tarayya a Amurka Hoto: BBC, Sahara Reporters and Nairametrics
Asali: UGC

1. Esther Agbaje

Ms Agbaje ta yi takara domin wakiltan gudunmar 59B a majalisar wakilai ta Minnesota a karkashin jam’iyyar Democrat. Ta lashe zaben da kuri’u 17,396.

Matashiyar mai shekaru 35 wacce ta karanci fannin shari’a a Harvard ta kayar da yar takarar jam’iyyar Republican, Alan Shilepsky da kuma ta jam’iyyar Green Party, Lisa Neal-Delgado a zaben.

Ta wallafa batun nasarar tata a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba a shafin Twitter.

2. Oye Owolewa

Haifaffen dan Najeriya a karkashin jam’iyyar Democrat, Oye Owolewa, ya lashe zaben kujerar dan majalisa mai wakiltan gundumar Columbia a kasar Amurka.

Bisa ga sakamakon zaben, Oye sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234 inda ya kayar da abokan karawarsa Joyce Robinson-Paul wanda ya sami kuri’u 15,541, da kuma Sohaer Syed wanda ya samu kuri’u 12,846.

Oye Owolewa mai shekaru 30, ya fito ne daga yankin Omu-Aran da ke jihar Kwara.

Ya kammala karatun digirin digir-gir dinsa a fannin Kimiyyar Harhada Magunguna daga Jami’ar Norteastern da ke birnin Boston a kasar ta Amurka.

KU KARANTA KUMA: Dan Najeriya ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai a Amurka

3. Nnamdi Chukwuocha

Nnamdi Chukwuocha ya sake lashe zabe a matsayin dan majalisar wakilai na Delaware daga gudunma ta 1.

A matsayinsa na dan jam’iyyar Democrat da bai da abokin hamayya, ya lashe kaso 100 na kuri’un wanda yayi daidai da kuri’u 7,640.

An zabi Chukwuocha domin ya wakilci gudunma ta 1 a majalisar wakilai ta Delaware a 2018.

Yana da digiri a kan ilimin tarihi da digiri na biyu kan aikin jama’a daga jami’ar jihar Delaware, yana da tarin sani kan siyasar cikin gida a jihar.

A gefe guda, 'Yar majalisar wakilai a Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zabenta a matsayin mai wakiltan mazabar Minnesota ta 5, Minneapolis, a jihar Minnesota.

Ihlan, 'yar shekara 38 ta doke abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican Lacy Johnson, wanda bakin fata ne kuma attajiri, da kashi 64.6% - 25.9% na kuri'u, Aljazeera ta ruwaito daga The Associated Press.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel