Gabanin 2027, ADC Ta Fada wa Tinubu Maganar da Za Ta Jefa Masa Tsoron 'Yan Adawa
- Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa kalaman Shugaba Bola Tinubu na cewa ba za a iya tsorata shi ba alamun nuna fargaba ne kawai a yanzu
- Halin ƙuncin rayuwa da rashin tsaro da ƴan Najeriya ke ciki sune dalilan da ya kamata su sanya shugaban ƙasar tsoron zaɓen 2027, in ji ADC
- Jam'iyyar ta zargi gwamnatin tarayya da rufe filayen taro domin hana ƴan adawa gudanar da harkokinsu na siyasa, abin da ta kira 'takurawa'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Jam’iyyar ADC ta mayar da zafafan martani ga furucin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cewa ba za a iya tsorata shi da barazanar ƴan adawa ba.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa kalaman shugaban suna nuna tsantsar fargaba da damuwa ne maimakon kwarin gwiwar da yake nuna wa a fili.

Source: Twitter
ADC ta caccaki Shugaba Bola Tinubu
Jam'iyyar ta zargi shugaban da kauce wa matsalolin da ke damun ƴan ƙasa kamar tsadar rayuwa da matsalar tsaro, inda ya fi mayar da hankali kan raddi ga abokan hamayyarsa na siyasa, in ji rahoton Vanguard.
Sanarwar ta ce yayin da iyalai ke fama da yunwa da hauhawar farashin kayayyaki, shugaban ya zaɓi yin ba'a ga ƴan adawa maimakon samar da mafita ga raɗadin da talakawa ke ciki.
A cewar ADC, akwai dalilai da dama da ya kamata su jefa shugaban ƙasa a cikin tsoro kafin babban zaɓen 2027.
Abin da zai hana Tinubu sukuni
Jam'iyyar ta nuna cewa ko a lokacin da shugaban yake wannan jawabi, akwai rahotannin sace ɗaliban da ke shirin zana jarabawar JAMB, wanda hakan ke nuna yadda rashin tsaro ya ƙara ta'azzara a sassan ƙasar nan.
Sanarwar ADC ta ce:
"Waɗannan sune dalilan da ya kamata su ba shi tsoro, domin mutane sun riga sun ƙudiri aniyar zaɓar canjin gwamnati a zaɓe mai zuwa."
Jam'iyyar ta ƙara da cewa tattalin arziƙin ƙasa na ci gaba da durƙushewa yayin da bashi ke ƙara yawaita, abin da ya sanya fatan ƴan ƙasa da dama ya fara dusashewa a ƙarƙashin jagorancin APC.

Source: Facebook
Zargin takura wa 'yan adawa
Haka kuma, ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta kira matsa wa ƴan adawa lamba ta hanyar hana su amfani da wuraren taron jama'a kamar filin Eagle Square.
Ta bayyana cewa babu wata gwamnati a baya da ta taɓa nuna irin wannan halin na hana jam'iyyun siyasa yin amfani da filayen da mallakin dukkan ƴan Najeriya ne ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
ADC ta tabbatar da cewa tana nan daram domin samar wa ƴan Najeriya sahihin canji da zai ceto su daga halin ƙunci da rashin tabbas, in ji rahoton Punch.
Rikici na neman barke wa a ADC
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan Kwankwasiyya sun maida martani ga Atiku Abubakar kan kalaman da ya yi game da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Kungiyar ta bayyana cewa Kwankwaso da Peter Obi ne kadai mutane ke goyon bayansu tsakani da Allah, ba don kudi ko tilasci ba.
Kwankwasiyya ta kuma yi fatali da ikirarin Atiku Abubakar cewa farin jinin Kwankwaso a Kano ya ragu, tana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

