Kalli jerin yan majalisan Republican 10 da suka yi watsi da jam’iyyarsu suka hade da Democrats wajen tsige Trump

Kalli jerin yan majalisan Republican 10 da suka yi watsi da jam’iyyarsu suka hade da Democrats wajen tsige Trump

- Majalisar wakilan kasar Amurka ta kafa tarihi wajen tsige shugaban kasa Donald Trump

- A wannan karon, harda yan jam'iyyar Trump na Republican 10 cikin wadanda suka tsige shi

- Tsigewar da aka yi wa shugaban ya biyo bayan zarginsa da aka yi da tunzura wasu magoya-bayansa har suka kai hari zauren Capitol

A ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, majalisar wakilan Amurka ta kafa tarihi yayinda ta tsige Shugaban kasa Donald Trump, karo na biyu a zango daya.

An tsige shugaban kasar Amurkan bayan ya zuga mabiyansa don su kai hari Capitol a kokarinsa na hana tabbatar da nasarar zababben Shugaban kasa Joe Biden.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna

Kalli jerin yan majalisan Republican 10 da suka yi watsi da jam’iyyarsu suka hade da Democrats wajen tsigge Trump
Kalli jerin yan majalisan Republican 10 da suka yi watsi da jam’iyyarsu suka hade da Democrats wajen tsigge Trump Hoto: Drew Angerer
Asali: Getty Images

Majalisar ta jefa kuri’u 232 cikin 197 don tsige Shugaban kasar. Sai dai, sabanin tsigewar farkon, yan jam’iyyar Republican 10 sun hade da yan Democrats wajen tsige shugaban kasar.

Ga jerin sunayen yan majalisan 10, kamar yadda CNN ya saki:

1. Adam Kinzinger

2. Liz Cheney

3. John Katko

4. Fred Upton

5. Jaime Herrera Beutler

6. Dan Newhouse

7. Peter Meijer

8. Anthony Gonzalez

9. Tom Rice

10. David Valadao

A baya mun ji cewa, Majalisar dokokin kasar Amurka ta tsige shugaban kasa, Donald Trump, a matsayin shugaba karo na biyu cikin wa'adinsa na farko.

KU KARANTA KUMA: Kukah: Jigon APC ya zargi JNI da kokarin hada rikicin addini, ya roki Buhari da Tambuwal su shiga lamarin

Trump yanzu ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige sau biyu.

A kuri'un da yan majalisan suka kada na tsigeshi, wadanda suka amince da a tsige Donald Trump sun samu rinjaye.

A wani labarin, mun ji a baya cewa Twitter ya bada sanarwar dakatar da wasu shafuka fiye da 70, 000 da ke da alaka da abin da ya kai ga aika-aika a zauren Capitol a kasar Amurka.

Ana zargin shugaba Donald Trump da tunzura wasu magoya-bayansa da shiga majalisar wakilan Amurka domin nuna adawarsu ga zaben da aka yi a 2020.

A ranar Juma’a, 8 ga watan Junairu, 2020, Twitter ya fara fatattakar rikakkun magoya bayan Donald Trump da ake amfani da su wajen tunzura al’umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng