Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka

Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka

- Atiku Abubakar, ya bayyana cewa akwai abun koyi a zaben da ya gabata na shugabancin kasar Amurka

- Atiku ya siffanta hukumomi masu karfin iko ke da ta cewa a demokradiyya ba masu daidakun masu iko ba

- Yayi kira da a dauki darasi daga zaben da ya gabata na kasar ta Amurka

Sa'anni kadan da suka shude majalisa ta tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bi sahun tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, wajen neman 'yan Najeriya su yi koyi da ka'idojin dimokuradiyya na Amurka.

Yana mai cewa 'manyan hukumomi masu karfin iko ba mutane masu karfin iko ba su ne tubalin kyawawan al'adun dimokiradiyya '.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC

Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka
Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka Hoto: UGC/Naira Metrics
Source: UGC

Ku tuna cewa Biden ya kayar da Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa na ranar 3 ga Nuwamba.

Trump ya yi zargin cewa Biden ya yi nasara ta hanyar magudin zabe da murdiya. Ya lissafa adadi mai yawa na jihohin da ya yi zaton an tafka magudi kuma ya tafi Kotun Koli ta kasar.

Gwagwarmayar da ya yi don shawo kan duniya cewa ya kayar da Biden a zaɓen an yi watsi da shi kamar yadda Majalisar Dokoki ranar Alhamis ta tabbatar da nasarar Biden.

Dangane da wannan, Atiku ya ce: “Dimokiradiyya, kamar yadda aka saba fada, tsari ne.

"Tare da kammala aikin tabbatar da kuri'ar zaben Joe Biden a matsayin Shugaban Amurka na gaba, a bayyane yake cewa cibiyoyi masu karfi suna da mahimmanci ga dorewar dimokiradiyya.

KU KARANTA: Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

"Wannan darasi ne da za a koya: cewa cibiyoyi masu karfi ba mutane masu karfi ba ne kariya daga kyawawan al'adun dimokiradiyya."

A wani labarin daban kuwa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tsarin zaben kasar ya fi na kasashen duniya ta uku muni.

Kasashen Duniya ta Uku sune kasashe masu tasowa na Afirka, Asiya, Latin Amurka, da Australia/Oceania.

Trump ya fadi haka ne ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba, don nuna adawarsa ga kayen da ya sha a hannun dan takarar Democrat Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Jaridar PUNCH a baya ta bada rahoton cewa Joe Biden na Jam'iyyar Democrat ya lashe zaben farko a zagaye na biyu na Georgia, sa’o’i kadan kafin a shirya Majalisa don tabbatar da zababben shugaban kasa a kan Donald Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel