Gwammati Ta Kinkimo Wa Mutane Aiki, Bashin N724,000 Ya Hau kan Kowane 'Dan Najeriya

Gwammati Ta Kinkimo Wa Mutane Aiki, Bashin N724,000 Ya Hau kan Kowane 'Dan Najeriya

  • Alkaluma daga Hukumar Kula da Harkokin Bashi ta Kasa (DMO) sun nuna cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa karshen 2025
  • Bincike ya nuna cewa idan aka raba wadannan kudade kan 'yan Najeriya, ana bin kowane mutum daya bashin kusan N724,000
  • Wani masanin harkokin kudi, Dakta Paul Alaje ya ce wannan bashin sai ya shafi har wadanda ba a haifa ba a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jimillar bashin da Najeriya ta ciyo daga ciki da wajen kasa ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025.

Hakan na nufin idan aka raba wadannan kudade kan 'yan Najeriya, kowane mutum daya ana bin shi bashin kusan N724,000, a cewar wani bincike.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin wani taro a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa alkaluman da Hukumar Kula da Bashi ta Ƙasa (DMO) ta fitar sun nuna cewa bashin ƙasar na ci gaba da ƙaruwa, musamman sakamakon yawaitar aro daga cikin gida.

Bashin da ake bin Najeriya na iya ƙaruwa

Rahoton ya nuna cewa wannan adadi bai haɗa da sabon bashin Naira tiriliyan 8.3 da aka amince da shi daga ƙasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Birtaniya ba, wanda hakan ke nufin bashin na iya ƙaruwa nan gaba.

A kiyasin da a kai baya-bayan nan, yawan jama’ar Najeriya sun kai kusan miliyan 220, hakan na nuna cewa kowane ɗan ƙasa na ɗauke da kaso mai tsoka na bashin ƙasa.

Yadda bashin Najeriya ya ƙaru

Bashin ya ƙaru daga Naira tiriliyan 153.29 a watan Satumba 2025 zuwa Naira tiriliyan 159.28 a watan Disamba 2025, wanda ke nuna ƙarin Naira tiriliyan 5.98 (kashi 3.9 cikin 100).

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan neman dawo da tallafin man fetur

A Dalar Amurka kuwa, bashin ya tashi daga Dala biliyan 103.94 zuwa Dala biliyan 110.97 a wannan lokaci, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Idan aka kwatanta da shekara guda, bashin ya ƙaru da Naira tiriliyan 14.61 (kashi 10.1 cikin 100), daga Naira tiriliyan 144.67 a Disamba 2024.

Najeriya ta ci bashi a gida da waje

Binciken ya nuna cewa bashin cikin gida shi ne mafi girma, yana da kaso 53.27 cikin 100 na jimillar bashin, inda ya kai Naira tiriliyan 84.85 zuwa watan Disamba 2025.

Gwamnatin tarayya ce ke riƙe da mafi yawan bashin cikin gida da ya kai Naira tiriliyan 80.49, yayin da jihohi da Babban Birnin Tarayya ke da Naira tiriliyan 4.36.

A ɓangaren bashin waje kuwa, ya kai Naira tiriliyan 74.43, wanda ke wakiltar kashi 46.73 cikin 100 na jimillar bashin. A Dala kuwa, bashin waje ya kai Dala biliyan 51.86.

Kara karanta wannan

Amurka ta cafke wasu ƴan Najeriya 8 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci? Gaskiya ta fito

Kudin Najeriya.
Wasu takardun N500 da mai POS ke kirgawa a wurin kasuwanci a Najeriya Hoto: Dan Kitwood
Source: Getty Images

Za a bar bashin ga ‘yan baya’

Masani kan harkokin kuɗi, Dakta Paul Alaje, ya bayyana cewa bashin da ake da shi a yanzu ba na ‘yan yanzu kaɗai ba ne, har ma da waɗanda ba a haifa ba za su biya shi.

Ya ce ƙarin bashin na nufin ƙarin kuɗin da za a rika kashewa wajen biyan bashin, wanda ake samu daga haraji da sauran kudaden shiga na gwamnati.

“Yayin da bashin ke ƙaruwa, haka ma kuɗin da za a biya yana ƙaruwa. Wannan yana ƙara wa tattalin arzikin ƙasa nauyi sosai,” in ji shi.

Tinubu zai sake cin bashin N8.3tn

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara bin matakan sake karbo wa Najeriya bashin kudin da suka haura Naira tiriliyan 8.

Kara karanta wannan

Naja'atu: Yadda ƴan Najeriya za su yi amfani da ADC a kifar da APC a 2027

Basussuka biyu da Tinubu ya bukaci Majalisar ta amince ya ciyo wa Najeriya sun kai Dala biliyan 6, kwatankwacin Naira tiriliyan 8.3 a kudin kasar nan.

A cewar shugaba Tinubu, bashin zai dauki tsawon shekaru 14 kafin a biya shi, ciki har da shekaru hudu na farko na jinkirin fara biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262