Jerin sunayen shugabannin Amurka da ba suyi tazarce ba

Jerin sunayen shugabannin Amurka da ba suyi tazarce ba

Za a kaddamar da Joe Biden na jam'iyyar Democrat, a matsayin wanda zai gaji Donald Trump a ranar Laraba, 20 ga Janairu. Za a rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 46.

Donald Trump, na jam'iyyar Republic, ya sha kaye a hannun babban abokin hammayyar sa, Joe Biden a yawan kuri'a da kuma kwalejin zabe.

Trump ba shi ne na farko da ya gaza yin tazarce ba, akwai wasu tsofaffin shugabannin Amurka da suka kasa yin tazarce a kujerar shugabancin Kasar.

Jerin shugabannin Amurka da ba suyi tazarce ba
Jerin shugabannin Amurka da ba suyi tazarce ba
Asali: Twitter

Wadannan su ne jerin shugabannin Amurka da ba su samu tazarce ba:

1. John Adams

John Adams ne shugaban Amurka na farko da ya fadi a zaben tazarce.

Shi ne mataimakin shugaban kasa na farko. Yayi mataimakin shugaban kasa karkashin shugaban Amurka na farko, George Washington, a 1789.

Bayan Washington ya kammala wa'adin zangon sa na biyu, Adams ya tsaya takara a jam'iyyar Federalist kuma ya lashe zabe.

DUBA WANNAN: Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

2. John Quincy Adams

Kamar dai John Adams, Quincy Adams bai samu nasarar yin tazarce a kujerar shugabancin Amurka ba. Shi ne babban dan shugaban Amurka na biyu kuma shugaban Amurka na shida.

An ruwaito cewa lokacin da yake shugaban kasa, ya samu sabani da jam'iyyun Democrat da Republic kuma hakan ya hana shi cimma nasarori.

3. Grover Cleveland da Benjamin Harrison

Martin Van Buren ne shugaba na gaba da ya fadi a zaben tazarce a 1840 amma Grover Cleveland ya ikirarin cewa faduwa zabe baya hana sake yin shugabancin kasar ba.

Cleveland, na Democrat, shi ne shugaban Amurka na 22 da 24 bayan lashe zabukan 1884 da 1892.

Shi ya sami mafi rinjayen kuri'u a shekarar 1888 amma ya sha kaye a hannun dan Republic Benjamin Harrison, wanda yayi shekara hudu.

4. William Howard Taft

Shi ne shugaban Amurka da ya fadi zaben tazarce bayan shekara 20 a shekarar 1912. Taft, na Republic, shi ne mutum daya tilo da ya rike mukumin shugaban Amurka da kuma alkalin alkalai na kasar Amurka.

Taft, yana shugaban kasa, ya ce bazai nada bakaken fata a ayyukan gwamnati ba tare da cire da yawan bakaken fata daga ofisoshin su a kudanci. Yayi shugabancin kasar daga 1909 zuwa 1913 kuma ya fadi a zaben 1912 inda ya sha kaye a hannun Woodrow Wilson.

5. Herbert Hoover

An zabe shi a matsayin shugaban Amurka a 1928 kuma yayi fama da matsalar taimakawa wajen sake gina kasar bayan faduwar kasuwar hannun jari a 1929.

Hoover yayi ta kokarin ganin ya haramta abubuwa da dama, duk da kokarin su tabbatar da haramcin giya a Amurka. Gwamnatin sa tayi fama da matsalar tattalin arziki a 1929, kuma iya tsawon lokacin yayi ta kokarin shawo kan matsalar.

KU KARANTA: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

6. George H W Bush

Shi ne shugaban Amurka na karshe da ya fadi zaben tazarce bayan ya sha kaye a hannun Bill Clinton, na jam'iyyar Democrat, a 1992. Bush ne shugaban Amurka na 41 kuma shi ne daraktan CIA daga 1976 zuwa 1980.

Yayi wa Reagan mataimakin shugaban kasa daga 1981 har 1989 lokacin da aka zabe shi don zama shugaban kasar, Bush ya shiga yake yake tare da sanya hannu a dokar ta zata hukunta nakasasu a 1990.

7. Donald Trumpn, dan shi, George W Bush ya zama shugaban Amurka kuma yayi wa'adi biyu kafin Barrack Obama ya maye gurbin sa a matsayin shugaban Amurka.

7. Donald Trump

An zabe shi a 2016 kuma yayi aiki daga Janairun 2017 zuwa Janairun 2021. Lokacin mulkin sa, Trump ya cire Amurka daga kungiyon duniya irin su Paris Climate Accords da WHO.

An tsige shi bisa nuna iko wajen janyo gwamnatocin kasashen waje game da zaben 2020, da kuma hada wata kungiya lokacin da ake binciken tsige shi.

Donald Trump ya sha kaye a hannun Joe Biden a zaben 2020 sai dai ya dauki watanni kafin yarda da faduwar.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164