Kaddamar da Sababbin Jiragen Kasa a Legas Ya Harzuka 'Yan Arewa
- Gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da sababbin jiragen kasa domin bunkasa harkokin sufuri, lamarin da ya jawo muhawara a tsakanin 'yan Arewa
- Daga cikin manya a Arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya fito ya yi magana game da sakacin da ya ce yankin ya yi a baya
- Haka zalika daruruwan mutane a Arewacin Najeriya sun yi korafi kan cewa an bar su a baya yayin da jihar Legas ta kama hanyar cigaba mai dorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
ihar Legas - Gwamnatin Jihar Lagos ta dauki wani muhimmin mataki na inganta sufuri ta hanyar kara sababbin jiragen kasa ga tsarin layin dogo na Red Line.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar a ranar Alhamis cewa jihar ta karbi wasu sababbin jiragen kasa masu dauke da tarago 24 domin karfafa ayyukan sufuri.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Amurka ta aika sako mai zafi, ta kafa sharadin komawa yaki da Iran

Source: Facebook
Gwamnatin Legas ta saye jiragen kasa
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan Legas ya bayyana yadda kaddamar da jiragen zai taimaka wa zirga-zirgar yau da kullum a fadin jihar.
“Mun karbi wasu sababbin jiragen kasa masu tarago 24 domin kara yawan jiragen Red Line na Lagos,”
In ji Sanwo-Olu.
Ya ce ana sa ran sayo jiragen kasan zai kara yawan daukar fasinjoji, tare da magance karuwar bukatar sufuri a cibiyar kasuwanci ta Najeriya.
Leadership ta rahoto ya ce:
“Wannan zai kara yawan daukar fasinjoji, rage lokacin jira da kuma saukaka zirga-zirgar yau da kullum ga mazauna Lagos,”
Korafin 'yan Arewa kan jiragen Legas
Manyan da kananan 'yan Arewa sun yi korafi game da yadda yankin ya rasa abubuwan more rayuwa kamar jiragen kasa da sauransu.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya yi korafi a shafinsa na Facebook da cewa:

Kara karanta wannan
Ana shirin tafiya Hajji, an fara barazanar tsayar da aiki da jiragen sama a Najeriya
"Legas kenan, Shekara takwas muna mulki, bamu tsinana komai ba, sai ci baya da jahilci. Ni kam na sha zagin yan Buhariyyah a lokacin."
Abban Sudais ya yi wa Gumi martani da cewa:
"To gwamnatin tarayya ce aka gaya maka ta yi wannan aikin. Matsalar Buhari ita ce bai ba ku kudi kun saka a cikin aljihunku ba."

Source: Facebook
Abdulrashid Adamu ya yi korafi da cewa:
"Gwamnonin Arewa sai auren zawarawa."
Umar Ibrahim Maigari ya bayyana cewa:
"Daga Abuja zuwa Kaduna ma guda daya ne tal, idan ya samu matsala ma sai a yi kwanaki ba ya aiki..."
Mohammed Aliyu ya ce:
"Ku tambayi gwamnonin Arewa, ina suke kai kudin a gwamnatin tarayya ke tura musu duk wata?"
Suleiman Billiyaminubb ya yi karin bayani da cewa:
"Ma sha Allah! An bar mu da rigima tsakanin mu. Masu sarauta fada, masu mulki fada, malamai fada, mabiya fada.
"Sai anyi magana muce ai Arewa sunfi kowa yawa. Amma Kuma yawan ya zama na shirme. Babu abin da yake tsakanin mana a Arewa sai hassada da mugunta.
"Shuwagabannin mu babu tunani sai satan kudi kawai shi ne a gaban su. Babu maganan inganta rayuwan al'umma, sai karya da surutu. Mabiya Kuma mun zama mabarata.
"Tabbas an yi mana nisa. Munanan an bar mu da masu garkuwa da mutane. Allah ya kyauta."
Maganar shugaban gwamnonin Arewa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya nemi a zabi Bola Tinubu a 2027.
Gwamnan ya bayyana cewa nasarar jam'iyyar APC a 2027 da tazarcen shugaba Bola Tinubu ne rufin asirin jama'ar da yake yi wa jawabi.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron siyasa da ya hada masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga karamar hukumar Akko a jihar Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
