APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari

APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari

- APC ta fidda sanarwar Allah wadai da tarzomar da ta faru a Capitol Hill a kasar Amurka

- Jam'iyyar ta bukaci shugaban kasar Amurka Donal Trump da ya yi koyi da Shugaba Muhammadu Buhari

- Jam'iyyar ta siffanta aika-aikar da ta faru da kokarin tauye tsarin demokradiyya

Jam’iyyar APC ta bukaci shugaban kasar Amurka Donald Trump da yayi koyi da takwaransa na Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), bayan faduwa zabe.

APC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ta Mai Kulawa da Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, “Amincin shugaba yana da muhimmanci kamar cibiyoyi masu karfi’.

Jam’iyyar ta kuma la’anci tarzomar Amurka ta Capitol Hill da masu zanga-zangar nuna goyon baya ga Trump suka yi kuma suka nuna adawa da kin Trump na amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasar Amurka na Nuwamba Nuwamba 2020.

KU KARANTA: Amurka: Sabuwar Korona ta sake kunno kai a jihohi takwas

APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari
APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce a wasu lokuta da Buhari bai gamsu da sakamakon zabe ba, ya garzaya kotu don a bi masa kadu.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa magoya bayan Trump sun kutsa kai cikin wani taron Majalisar da aka gudanar a ranar Laraba domin tabbatar da nasarar zaben Joe Biden.

Kutsa kan ya haifar da rudani da tashin hankali da ba a taba ganin irin sa ba a tsarin dimokradiyyar Amurka da kuma zargin shugaban na yunkurin juyin mulki.

Magoya bayan Trump sun yi cincirindo, suna kutsawa ta cikin ofisoshi da kuma kan manya-manyan majalisun dokoki a Capitol Hill.

Akalla mutane biyar sun mutu a cikin tarzomar da ake zaton shugaban Amurka ne ya iza wutar.

Sanarwar ta ce, “Abubuwan da suka faru a a awuwi 72 da suka gabata a Amurka shine a ce mafi karancin abin zargi. Yawancin lokaci, ana amfani da zaɓen Amurka a matsayin tushen duba game da zaɓuka a wasu ƙasashe na dimokiradiyya.

“An amince da cewa cibiyoyi masu karfi suna da tushe ga rayuwar dimokiradiyya. Koyaya, wannan zaɓen na Amurka yana ƙarfafa gaskiyar cewa amincin shugaban ƙasar yana cika ayyukan waɗannan cibiyoyin.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takara kuma ya fadi zabe sau biyu sannan ya bi tsarin har Kotun Koli kan dukkan zabuka biyun. Wannan alama ce ta fice ta dimokiradiyya ta gaskiya.

“Bayan samun nasara a karshe a 2015, gwamnatin da APC ke jagoranta ta gudanar da gyare-gyare na asali don karfafa hukumomin mu.

Sakataren ya bayyana cewa mulkin APC ta bai wa INEC cikakken ikon gunadarwa don karfafa cibiyoyin gudanarwa a kasar.

KU KARANTA: Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

Akpanudoedehe ya yi fatali da sanarwar jam’iyyar PDP inda ya gargadi Buhari da APC da su amince da shan kaye idan aka kayar da su a babban zaben 2023.

Ya ce, “Wannan ya yi nisa daga zamanin siyasar ko-ta-kwana ta PDP, inda fararen hula suka karbe ragamar jami’an tsaro don murkushe son jama’a da kuma tantance sakamakon zabe.

Sakataren ya nuna rashin jin dadinsa tare da Allah wadai da abin da ya faru a Amurka.

A wani labarin, Jam’iyyar APC ta ce tana shirin yin rajistar mambobi miliyan 2 a Adamawa a ci gaba da rajistar membobin da ke gudana a duk fadin kasar, Vanguard ta ruwaito.

Farfesa Tahir Mamman, memba Mai Kula da Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taro na APC ya fadi haka ne a wani taron manema labarai ranar Asabar a Yola.

“Muna so mu ga akalla mazauna Adamawa miliyan biyu a matsayin mambobi masu rajista na jam'iyyar APC a cikin rajistar membobin da ke gudana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.