Jerin manyan kyaututuka masu tsada 10 da aka yi wa Donald Trump
Duk da cewa mulkin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump cike ya ke da abubuwa masu janyo cece-kuce, akwai Amurkawa da suka yaba da irin jagorancin da ya yi wa kasar.
A cikin wannan rubutun, Legit.ng ta lissafo manyan kyautuka 10 da aka yi wa Trump kamar yadda aka wallafa a wani rahoton Business Insider.
Ga jerin kyautukan da wadanda suka bayar tare da darajar abinda suka bada kyauta:
1. Damarar (belt) Zakaran Dambe wanda Colby Covington ya yi masa kyauta ($650)
2. Championship belt daga Randy Jackson ($2,995)
3. Tagulla da ke nuna Dutsen Mount Rushmore na kasar Amurka daga Honarabul Kristi Noem, Gwamnan Jihar South Dakota ($1,100)
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi
4. Tagulla da ke tuta a samar Iwo Jima daga Timothy Davis, Shugaba kuma wanda ya kafa gidauniyar Greatest Generations ($25,970)
5. Kwamfuta ta Mac Pro (wacce aka fara kera wa a Flex Factory da ke Austin Texas) daga Shugaban kamfanin Apple, Tim Cook ($5,999).
6. Rigar fata daga Bill Ford, Shugaban Kamfanin Ford Motor ($529)
7. Sandar buga wasar kwallon Golf da murfinta mai dauke da sunan Trump daga Bettinardi Golf ($769)
8. Sandar Golf da murfinta daga Allen Simon ($625)
9. Sandar Golf mai dauke da suna daga Dennis Muilenburg, Shugaban kwamitin masu gudanarwa na Boeing ($499)
KU KARANTA: Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka
10. Sandunan golf, murafensu, jakar saka kayan golf da lema daga DerekSprague, Shugaban kungiyar masu buga wasar Golf na Amurka ($1,285)
Jimillar kudin kyauttutukan da aka yi wa Trump ya kai kimanin $40,421. Hakan ya kai kimanin N15,319,599 a kudin Nigeria idan an yi canji da darajar Naira da Dallar Amurka na CBN a yanzu wato N379 - $1.
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng