Rikici na Neman Barkewa a ADC, 'Yan Kwankwasiyya Sun Yi Wa Atiku Tatas kan Kwankwaso
- 'Yan Kwankwasiyya sun maida martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan kalaman da ya yi game da Kwankwaso
- Kungiyar ta bayyana cewa Kwankwaso da Peter Obi ne kadai mutane ke goyon bayansu tsakani da Allah, ba don kudi ko tilasci ba
- Kwankwasiyya ta kuma yi fatali da ikirarin Atiku cewa farin jinin Kwankwaso a Kano ya ragu, tana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ke nuna cewa tasirin siyasar Rabiu Musa Kwankwaso a Kano ya ja baya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsere da fafutukar neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin hadakar jam’iyyun adawa ta ADC.

Source: Facebook
Magoyan bayan Obi da Kwankwaso
Aminiya ta tattaro cewa 'yan Kwankwasiyya sun ce ikirarin Atiku ba gaskiya ba ne, suna mai cewa mutum biyu kacal ne ke da mabiyan da ke kaunarsu da zuciya a fadin kasar nan, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Mai magana da yawun Kwankwasiyya, Hon. Habib Mailemo, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi a tashar Trust TV.
Ya ce mabiyan da Obi da Kwankwaso ke da su ba kudi aka ba su ba, sai dai sun samu irin wannan soyayya ne sakamakon yakinin jama’a da kwarewar shugabancin da suka nuna a baya.
“Peter Obi da jagorana, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, su ne kadai ke da mabiyan da ba a sayensu da kudi. Jama’a sun yarda da su ne saboda kwarewarsu da irin ayyukan da suka yi,” in ji shi.
Kwankwasiyya ta ja hankalin 'yan ADC
Ya kara da cewa ya kamata tattaunawar siyasa a ADC ta karkata daga batun wanda ya fi karfi zuwa ga yadda za a ceto Najeriya daga halin da take ciki.
A cewarsa, shiga hadakar jam’iyyun adawa da Kwankwaso ya yi na da manufa guda ne kawai, watau taimakawa wajen ceto kasar nan.
“Jagorana ya bayyana karara cewa ya shiga wannan hadaka saboda yana son bayar da gudunmawa wajen ceto Najeriya,” in ji shi.
Kwatanta Atiku da Kwankwaso
Da yake mayar da martani kan batun wanda ya fi tasirin siyasa a Arewa, Mailemo ya amince cewa Atiku ya dade yana siyasa, amma ya ce nasarorin da ya samu a baya sun dogara ne da goyon bayan jam’iyya da manyan ‘yan siyasa.
“Gaskiya ne Atiku ya taba takara sau da dama, musamman a PDP inda yake da goyon bayan gwamnoni da tsarin jam’iyya mai karfi. Amma ba zai iya danganta kuri’un da ya samu da karfinsa na kashin kai kadai ba,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa bambancin da ke akwai shi ne, Obi da Kwankwaso sun gina tasirinsu ne da kansu ba tare da dogaro da manyan tsare-tsaren jam’iyya ba.
A karshe, ya ce idan ana son a yi kwatance mai adalci da Atiku, dole ne a gwada shi a irin yanayin da bai samu cikakken goyon bayan manyan ‘yan siyasa ba.

Kara karanta wannan
Iran ta amince da bukatar Amurka, ta canza shawara kan batun kera makamin nukiliya
Atiku ya kare kansa daga cin hanci
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiki Abubakar, ya kare kansa kan yawan danganta shi da zargin cin hanci da rashawa da ake yi.
Atiku ya bayyana cewa Olusegun Obasanjo, ya taɓa ba da izinin kafa wani kwamiti domin bincikarsa lokacin da yake kan mulki amma ba a iya gano komai ba.
Ya ci gaba da cewa zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka biyo shi tsawon shekaru sun samo asali ne daga siyasa maimakon kwararan shaidu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

