Rep. Taylor Greene ta jefi Biden da zargi masu karfi, tana so a tsige Shugaban kasa

Rep. Taylor Greene ta jefi Biden da zargi masu karfi, tana so a tsige Shugaban kasa

- Da alamu magoya bayan Donald Trump suna neman kawowa Joe Biden matsala

- Marjorie Taylor Greene ta kawo maganar tsige sabon shugaban kasar Amurkan

- ‘Yar Majalisar ta na zargin Biden da aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi

Rahotannin da su ke zuwa daga kasashen waje sun bayyana cewa wata ‘yar majalisar wakilai a Amurka, ta bukaci a tsige shugaban kasa Joe Biden.

‘Yar majalisar da ke wakiltar yankin Arewa maso yammacin Georgia, Misis Marjorie Taylor Greene, ta kawo maganar tsige Joe Biden a ranar Alhamis.

Marjorie Taylor Greene ta bada wannan sanarwa a shafinta na Twitter, ta ce: “Yanzu na gabatar da kudirin tsige Joe Biden, za mu ga yadda za ta kaya.”

Har ila yau, Taylor Greene ta fitar da jawabi inda ta zargi shugaba Joe Biden da aikata rashin gaskiya, wanda su ka hada da hada-kai da kasar Ukraine.

KU KARANTA: Joe Biden ya rattaba hannu a kan sababbin dokoki 17 a Amurka

‘Yar majalisar ba ta tsaya nan ba, ta zargi ‘dan shugaban kasar, Hunter, da karbar kudi daga hannun manyan makiyan Amurka watau kasashen Rasha da Sin.

A cewar ‘yar adawar, Biden bai cancanci ya mulki Amurka ba, ta zarge shi da cin amanar ofis a lokacin da yake rike da kujerar mataimakin shugaban kasa.

Misis Marjorie Taylor Greene ta ce Biden ya fifita lamarin ‘dansa a lokacin da ya ke mulki.

“Shugaba Biden ya nuna zai yi duk abin da ta kama domin ya ceci ‘dansa, Hunter, ya shakawa danginsa dukiya daga kudin miyagun kamfanoni.” Inji Greene.

KU KARANTA: Me Donald Trump ya fada kafin ya bar mulki?

Sai dai Greene mai shekara 46 ta yi kaurin-suna a kwanakin nan wajen yada labaran bogi a shafukan sada zumunta, ta na cikin ‘yan a mutun Donald Trump.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban kasa.

Kun samu labari cewa 'ya 'yan tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump sun gaza rika hawaye yayin da Mahaifinsu yake jawabinsa na karshe a mulki.

Shi ma sabon shugaban kasa Joe Biden ya yi kuka da ya ke sallama da mutanen Delaware, daga baya Biden fadi dalilin da ya sa aka gan shi ya na sharara hawaye.

Biden ya yi kuka a fili ne bayan ya tuna da babban 'dansa da ya rasu shekaru biyar da su ka wuce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel