Siyasar Najeriya
Gwamna Alex Otti na jihar Abia, ya bayyana dalilin kauracewa gidan gwamnati da ke Umuahia, sai dai ya yi aiki daga gidansa na kashin kansa da ke Umuehim Nvosi.
'Yan majalisar jiha a Kebbi sun bayyana sauya sheka zuwa APC a daidai lokacin da ake ci gaba da kuka da yadda jam'iyyar APC ke yiwa 'yan kasar nan gashi.
'Yan majalisar dokokin jihar Kebbi guda uku da aka zaba a inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar. Sun samu tarba mai kyau.
A makon nan ne kwatsam aka ji yadda Rarara ya saki sabuwar da ke yabawa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu duk da halin da ake ciki na yunwa da fatara a Arewa.
An kawo maku sunayen 'yan majalisar tarayyar da mutuwa ta raba da mazabunsu. A ciki akwai Ifeanyi Uba wanda Sanata ne da Isa Dogonyaro da Abdulkadir Jelani Danbuga.
Tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi 23 da aka sallama sun yi barazana ga Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers kan kin bin umarnin Kotun Koli.
Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar SDP na kasa, ya lissafa mutane biyar da ke rike da gwamnatin shugaba Bola Tinubu. Gabam ya ce idan Tinubu ya gaza su ne sila.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa ba zau bar APC matukar Gwamna Babagana Zulum na cikinta, ya bayyana cewa da shi aka kafa jam'iyyar tun asali.
Gwamnan Seyi Makinde ya aika da wasika ga majalisar jihar Oyo inda ya sanar da su kudurinsa na tafiya hutu tare da mika mulki ga mataimakinsa Bayo Lawal.
Siyasar Najeriya
Samu kari