Bidiyo: Ƴan Najeriya Sun Maida Martani Yayin da Mataimakin Tinubu da Ministoci Suka Ziyarci Buhari
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar ƙusoshin gwamnati sun kai ziyara ga Muhammadu Buhari a Daura
- Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ya wallafa bidiyon wannan ziyara a shafinsa na soshiyal midiya ranar Asabar
- Ziyarar dai ta haddasa kace-nace tsakanin ƴan Najeriya, inda wasu ke sukar jagororin tare da nuna cewa bai kamata ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Daura, jihar Katsina - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa da ya gabata, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ne ya wallafa bidiyon ziyarar a shafinsa na manhajar X watau Twitter ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2024.
Ahmad ya ce Shettima ya jagoranci manyan ƙusoshi, "da suka haɗa da ministoci, Sanatoci da wasu jiga-jigan gwamnati," zuwa wurin tsohon shugaban ƙasar a Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin shugaban ya wallafa cewa:
"Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima tare da babbar tawagarsa ta ministoci, sanatoci da manyan jami'ai sun ziyarci tsohon shugaban ƙasa Buhari da yammacin nan a gidansa na Daura, jihar Katsina."
Martanin ƴan Najeriya kan ziyarar da Shettima ya kai wa Buhari
Duk da Bashir Ahmad bai yi cikakken bayani kan ziyarar ba amma bidiyon da ya wallafa ya ja hankalin ƴan Najeriya da dama.
Ibrahim, @abbanarfat10 ya ce:
"Na kasa fahimtar meyasa suke zuwa gidansa, watakila shiyasa tsarin tattalin arzikin mu ke tangal-tangal kamar sabis ɗin Glo."
jof, @jofamilugba ya ce:
"Sun kai ziyara ga mutumin da suke ta ɓaɓatun ya bar mataccen tattalin arziki, ƙila sun je kara ɗauko darasin yadda zasu ƙarisa mana tattalin arzikin ƙasa ne."
Adeleye jeremiah, @Jerrycaffe ya maida raddi ne ga Bashir Ahmad, yana mai cewa:
"Menene girma a tattare da wannan tawagar? Ba abun da suke tsinanawa a kan mulki."
Shi kuma Olu, @MrOlubabs's ya maida hankali ne kan kayan da ke falon tsohon shugaban kasa Buhari, inda ya ce:
"Baba fa ya sauya kujeru, Allah mun gode maka."
Ma'aikata zasu samu tallafi mai gwabi a Yobe
A wani rahoton na daban Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ware kuɗi N4.1bn domin tallafawa ma'aikata da ƴan fansho saboda tsadar rayuwa.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban ma'aikatan jihar Yobe, ta ce Buni ya amince da ƙarin N10,000 ga ma'aikata da N5,000 ga ƴan fansho.
Asali: Legit.ng