Yadda Atiku Ya Kusa Zabar Tsohuwar Minista a Matsayin Abokiyar Takara a 2027

Yadda Atiku Ya Kusa Zabar Tsohuwar Minista a Matsayin Abokiyar Takara a 2027

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya zabi Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa
  • Kafin zabar Amaechi, an gudanar da shawarwari kan mutumin da ya kamata a zaba ya zama mataimakin Atiku
  • Daga cikin mutanen da aka tuntuba don zama abokan takarar Atiku har da tsohuwar Ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Atiku Abubakar ya yi shawarwari kafin zabar Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

An bayyana cewa wasu dabarun siyasa na bayan fage sun fito fili game da yadda a karshe aka cimma wannan zaɓi na Amaechi.

Atiku ya duba mutane da dama kafin zabar Amaechi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Wasu majiyoyi a jam'iyyar, sun sanar da jaridar Tribune cikakkun bayanai kan abubuwan da suka faru wajen zabar abokin takarar Atiku.

Mutanen da aka duba

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kai karar jigon ADC kotu, ya nemi N8bn kan zargin bata suna

A cewar majiyoyin, wasu na kusa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar sun yi lissafin cewa mafi kyawun yankin da za a ɗauko abokin takara gabanin zaben shekarar 2027 shi ne Kudu maso Gabas.

An gano cewa a cikin wani ƙoƙari na fari-da-fari na tabbatar da cewa ɗan takara daga Kudu maso Gabas ya cike gurbin, an gabatar da sunaye da dama, waɗanda suka haɗa da Sanata Ben Obi; Hon. Emeka Ihedioha, da kuma tsohuwar Ministar kuɗi, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

Wata majiyar ta daban ta bayyana cewa an yi muhawarar cewa idan har ɗan takara daga Kudu maso Gabas ba zai yi aiki ba, to kamata ya yi a duba tsohon aminin Atiku na daɗewa kuma tsohon gwamnan jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke.

An gano cewa wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun yi amanna cewa rashin kasancewar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, a kan tikiti daya da Atiku, ya sa ya zama dole a nemo wani babban suna daga Kudu maso Gabas domin gurbin mataimakin shugaban kasa.

Atiku ya tura tawaga ga Ngozi Okonjo-Iweala

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

Majiyoyin sun ƙara da cewa yayin da shugabannin jam'iyyar ke tsaka da tace sunayen fitattun mutane daga jerin sunaye masu tsawo, an aika da wata tawaga ƙarƙashin jagorancin wani babban jigo a jam'iyyar daga shiyyar Arewa maso Gabas zuwa gurin Okonjo-Iweala lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarta.

An gano cewa yayin da aka nuna ziyarar kamar ta taya murna ce ta taron zagayowar ranar haihuwa, jagoran tawagar, wanda tsohon babban jigo ne a PDP, wanda kuma ya taɓa komawa jam'iyya mai mulki ta APC a wani mataki, ya gana da Okonjo-Iweala domin tattauna ajandar.

Wata majiya ta bayyana cewa Okonjo-Iweala bada gamsashshiyar amsa ba game da shirin, amma ta shawarci tawagar da su gudanar da tuntuɓar juna mai faɗi a Najeriya kafin su tsayar da zaɓi.

An yi shawarwari kafin zabar Amaechi

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa:

“Shawarar ADC ta zaɓar Amaechi bai kasance abu mai sauƙi ba kamar yadda ya bayyana. Ko da yake ya bayyana a matsayin zaɓinsu mafi kyau tun farko, duba da cewa shi ne ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani kuma shi ne fitaccen ɗan takara daga Kudancin ƙasar."

"Sai dai kuma, wasu jiga-jigai a cikin jam'iyyar sun yi amanna cewa ɗan takara mai asali daga Kudu maso Gabas zai fi yi wa jam'iyyar amfani."

Kara karanta wannan

ADC ta tabbatar da abokin takarar Atiku bayan fara gunaguni kan zabin Amaechi

“Sakamakon haka, sun tsara wata ajanda ta lallabo Okonjo-Iweala cikin takarar a matsayin abokiyar takarar Atiku.”

“Wani babban jigon siyasa daga Arewa maso Gabas ya jagoranci tawaga domin ziyartar tsohuwar Ministar, domin yi mata bayani kan halin da ake ciki. Mun fahimci cewa matar ba ta ba da amsa ta tabbatacciya ba, amma an ce ta ba da shawarar cewa tawagar ta bincika sosai kuma ta yi tuntuɓar juna ta gari a faɗin yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu gabanin zaɓen.”

Atiku ya zabi Amaechi matsayin abokin takara
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

Majiyar ta ce yayin da ake tsaka da gudanar da dukkan waɗannan shawarwari, Atiku ya kasance yana tuntuɓar Amaechi akai-akai, lamarin da ya kai ga samun sauƙin tsarin a ƙarshen al'amura.

Atiku ya soki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu daya daga cikin Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan, da ya yi yunkurin soke rajistar jam’iyyun adawa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na son raunana jam’iyyun adawa gabanin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng