Fada Zai Dawo: Trump Ya Yi Gargadi Mai Tsauri kan Iran duk da Maganar Sulhu
- Yayin da ake maganar sulhu tsakanin Amurka da Iran, Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa kasar za ta iya sake ɗaukar matakin soja
- Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hare-hare kan wuraren ajiyar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, tare da cibiyoyin radar da ke bakin teku
- Ya yi barazanar cewa idan Iran ta ci gaba da hare-harenta, Amurka za ta dauki mataki, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta ci gaba da wanzuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaba Donald Trump ya sake yin gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yakin da ake yi.
Trump ya yi gargadin cewa har yanzu Amurka na iya ƙara ɗaukar matakin soja kan Iran bayan sababbin hare-haren da sojojinta suka kai kan wasu wuraren Iran.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, a yau Lahadi 28 ga watan Yunin shekarar 2026 da muke ciki.
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran
Wannan na zuwa bayan cimma yarjejeniya domin tsagaita wuta a yakin da ake yi wanda ya shafe fiye da watanni uku a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar za su dakatar da duk wani harin kare-kai kan Amurka da Isra'ila.
Majalisar ƙolin tsaron ƙasa ta Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "nasara ga al'ummar Iran" tare da gargaɗin Amurka kan sake yin wani kuskuren.
Iran ta yi iƙirarin cewa Amurka ta amince da haƙƙinta na tace sinadarin nukiliya a matsayin wani ɓangare na tattaunawar tsagaita wuta da za a yi.

Source: Getty Images
Barazanar da Trump ya yi kan kasar Iran
Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hare-hare kan wuraren ajiyar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, tare da cibiyoyin radar da ke bakin teku.
Ya ce hare-haren sun biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin wani sabon karya yarjejeniyar tsagaita wuta daga Iran, yana mai zargin Tehran da ci gaba da ɗaukar matakan tada rikici.
Trump ya yi gargaɗin cewa idan Iran ta ci gaba da irin waɗannan matakai, Amurka "za ta tilasta ta kammala aikin ta hanyar soja," sannan ya ƙara da cewa:
"Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta ƙara wanzuwa ba."
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Amurka
Mun ba ku labarin cewa Iran ta kai hare-haren ramakon gayya kan wuraren da ke da alaƙa da sojojin Amurka bayan hare-haren saman da Amurka ta kai Tehran.
Iran ta kuma ƙaddamar da hare-hare da jiragen yaki zuwa kasar Bahrain bayan ta farmaki wani jirgin dakon da ya so wucewa ta mashigar Horrmuz.
Yayin da rikici ke son dawowa Gabas ta Tsakiya, gwamnatin Bahrain ta sanar da cewa harin babbar barazana ne ga tsaron ƙasar da mazauna cikinta.
Asali: Legit.ng

