Meye Gaskiyar Cewa an Fasa Rumbun Abinci Na NEMA a Abuja? Gaskiyar Batu Ya Fito Daga Tushe

Meye Gaskiyar Cewa an Fasa Rumbun Abinci Na NEMA a Abuja? Gaskiyar Batu Ya Fito Daga Tushe

  • Hukumar agaji ta NEMA ta musanta ikirarin cewa wasu ‘yan daba sun daka wawa a a wani dakin ajiyar kayan abinci ta da ke Abuja da safiyar Lahadi
  • Mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Manzo Ezekiel, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ma’ajiyar ba ta da alaka da hukumar.
  • Sai dai an tabbatar da cewa rumbun ajiyar da aka wawashe mallakin sashen noma na babban birnin tarayya ne

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce rahoton da aka samu na cewa wasu mahara sun kutsa rumbun ajiyar abinci da ke Abuja, babban birnin Najeriya, a ranar Lahadi, 3 ga Maris, karya ne.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Mutane sun fasa dakin ajiya, an sace buhunan abincin gwamnati a Abuja

A wani sako da kakakin hukumar, Manzo Ezekiel ya fitar a shafinsa na X, ya ce gidan ajiyar da aka wawashe da aka gani a wani faifan bidiyon ba shi da alaka da hukumar NEMA.

Ya kuma nuna damuwa da jajantawa masu wannan dakin ajiya da aka wawashe a yanayi irin wannan.

Gaskiyar batun fasa rumbun abinci na NEMA a Abuja
Batu kan fasa rumbun NEMA a Abuja | Hoto: NEMA Nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanne rumbun ajiya aka wawashe a Abuja?

Kamar yadda gidan Talabijin na Channels TV ya ruwaito, wasu ‘yan daba a Abuja sun kutsa a wani dakin ajiya na sashen noma na babban birnin tarayya Abuja.

An ruwaito yadda suka wawashe kayan abinci da sauran kayayyakin da aka ajiye a wurin mai tarin yawa.

Kakakin sakatariyar noma ta FCT ya tabbatar da cewa, rumbun ajiyar da aka wawashe na hukumar ne a wani sako da ya aikewa manema labarai domin amsa tambayoyinsu a yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka fi dadin zama a duniya, ita ce ta 8 a Afrika

Jami’in hulda da jama’a na sakatariyar noma na babban birnin tarayya Abuja, Zakari Aliyu, ya tabbatarwa da Channels Tv ta hanyar sakon kar-ta-kwana cewa rumbun ajiyar da aka wawashe na hukumarsu ne.

Ga dai abin da ya rubuta a shafin X:

Yadda aka fasa rumbu a jihar Bayelsa

A watan Agustan bara ne aka samu wasu tsagerun da suka fasa rumbun abinci a wani yankin jihar Bayelsa a Kudancin Najeriya.

Rahoto ya bayyana cewa, fasa rumbun ya jawo asarar miliyoyi ga wadanda suka mallaki rumbun, wanda aka ce na gwamnati ne.

Tun bayan da aka cire tallafin man fetur a kasar nan kayayyaki suka fara tashin gauron zabi, jama’a na kukan yunwa a kowanne yanki na kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel