Kungiyar Fulani Ta Miyetti Allah Ta Nemi a Kame Dan Fafutukar Raba Najeriya Gida Biyu

Kungiyar Fulani Ta Miyetti Allah Ta Nemi a Kame Dan Fafutukar Raba Najeriya Gida Biyu

  • Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta nemi a kamo Sunday Igboho, dan awaren kabilar Yarbawa
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Igboho ke ci gaba da furta kalamai masu nuna kiyayya ga al’ummar Fulani
  • A baya, an tsare Igboho a kasar waje bisa zarginsa da wasu laifukan da suka shafi shiga kasa ba tare da izini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN ta yi kira da a kamo mai adawar awaren Yarbawa, Sunday Igboho.

Wannan kiran dai martani ne ga wani faifan bidiyon da ya yadu, inda aka ga Igboho na furta kalamai masu tada hankali, inda ya bukaci a kori Fulani makiyaya daga kasar Yarbawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dura kan 'yan Crypto, ta kakaba wa Binance tarar dala biliyan 10

A cikin faifan bidiyon, Igboho, wanda ya yi kaurin suna wajen munanan kalamai, ya bayyana da kakkausar murya kan aniyarsa ta fatattakar Fulani makiyaya daga yankin Kudu maso Yamma.

MACBAN ta nemi a kame mai fafutukar kafa kasar Yarbawa
MACBAN ta nemi a kama Sunday Igboho | Hoto: RealSundayIgboh (X), Miyetti Allah - MACBAN (Facebook)
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MACBAN ta nemi a kame Igboho

Ya bayyana zargin yadda kabilun Fulani suka zama masu tada zaune tsaye tsakanin kabilun yankin, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban MACBAN na kasa, Baba Othman Ngelzarma, an bayyana cewa, kalaman Igboho sun yi kaushi kuma za su jefa al’umma cikin fargaba.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana tsoron cewa, lamarin zai iya janyo martani daga bangarori daban-daban a kasar nan, rahoton Sahara Reporters.

Kalaman shugaban MACKBAN kan kamo Sunday Igboho

A cewar shugaban:

“Muna kira ga shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu da sauran hukumomin tsaro da su kame tare da gurfanar da Sunday Igboho bisa furta kalamai masu tada hankali da ke daidai da cin amanar kasa saboda burinsa na tabbatuwar kasar Oduduwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

“Maganganunsa sun sabawa doka. Idan har za a tsare Nnmadi Kanu bisa irin wannan laifin, babu dalilin barin Sunday Igboho ya ci gaba da yawo ba tare da an kame da gurfanar dashi ba.”

MACBAN ta yi amanna da zaman lafiya, inda ta yi kira ga yaki da kabilanci da tada zaune tsaye daga kungiyoyi har kan daidaikun mutane.

An kama Sunday Igboho a baya

A wani labarin, kun ji yadda aka kama Sunday Igboho a Cotonou bayan da ya shiga kasar ba tare da ka'ida ba.

An ruwaito cewa, yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Jamus ne a lokacin da aka yi ram dashi a kokarin fecewa.

Kafin barinsa Najeriya, an ce jami'an hukumar DSS sun yi kokarin kame shi, lamarin da bai kai ga nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel