Abin da Ya Sa Bola Tinubu da APC Suke Tsoron Atiku Abubakar a Takarar Shugaban Kasa

Abin da Ya Sa Bola Tinubu da APC Suke Tsoron Atiku Abubakar a Takarar Shugaban Kasa

  • Idan akwai wanda zai iya doke Bola Ahmed Tinubu idan an zo takara, wasu suna ganin wannan mutumi shi ne Atiku Abubakar
  • Irinsu Adnan Mukhtar Adam Tudunwada sun bukaci jam’iyyar PDP ta tsaida Wazirin Adamawa sannan a mara masa baya
  • Adnan ya fadawa Legit Atiku yana da ilmin tattalin arziki kuma yana da kudin yakin neman zabe a doke jam’iyya da ke mulki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Tun yanzu wasu sun fara buga gangar siyasa, ana ganin ya kamata a karbe mulki daga hannun Bola Ahmed Tinubu.

Kwamred Adnan Mukhtar Adam Tudunwada matashin ‘dan siyasa ne kuma wanda yake goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar
Jagoran adawa kuma jigon PDP, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku: Legit ta zanta da Adnan Tudunwada

Kara karanta wannan

2027: An cigaba da kiran Kwankwaso da Obi su goyi bayan Atiku a kifar da Tinubu

Legit ta zanta da wannan ‘dan siyasa, inda ya shaida mata cewa Wazirin Adamawa shi ne ya fi dacewa da yin takara a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da Atiku ya yi takara a 2019 da 2023 babu nasara ba, Adnan Mukhtar Adam Tudunwada yana so a sake ba sa tikiti.

Ko da jam’iyyar PDP ta tsaida wani ‘dan takara na dabam a 2027, Adnan Tudunwada ya ce da wahala ya iya doke Bola Tinubu.

"Shi ne mai karfi daga Arewa, shi kadai ne wanda a zahiri ta nuna yana da zuciya."
"Yana da arziki, babban ‘dan kasuwa ne kuma takarar kujerar shugaban kasa sai da kudi a Najeriya."
"Mun ga yadda aka yi da Muhammadu Buhari, sai da sauran ‘yan siyasa suka mara masa ya kai labari"

- Adnan Mukhtar Tudunwada

Adnan: "Atiku ya san tattalin arziki"

Kara karanta wannan

"Dino ya tsallake": Tsohon sanatan PDP ya saki satifiket din tsira daga hannun Tinubu

Tsohon ‘dan takaran kujerar majalisar dokokin yake cewa Atiku shi ne wanda kowa yake tsoro a APC saboda an san cancantarsa.

Baya ga haka, Adnan ya yabi gwaninsa da sanin tattalin arziki kamar yadda ya saba ba gwamnati mai-ci shawararin kawo gyara.

“Cigaba ne a rika daukar shawarar adawa kuma aka rika yin adawa da ilmi ta manufofi ba taba mutunci ba.”

- Adnan Mukhtar Tudunwada

Malamin makarantar ya ce Atiku ya fito da tsare-tsaren da zai bi kafin cire tallafin fetur, akasin garajen da shugaba Tinubu ya yi.

A cewar Adnan, za a samu mafita idan borin kunya bai hana a karbi shawarar Atiku ba.

Atiku Abubakar bai tsufa da takara ba?

Ana kukan Atiku zai yi tsufa da shugabanci a shekara 80, amma shi kuwa Adnan yana ganin an saba ganin dattawa a kan mulki.

A zantawarmu ya bada misali da shugabannin Amurka kamar Joe Biden da Donald Trump.

Kara karanta wannan

Masoya sun fara zuga Farfesa Isa Ali Pantami ya fito takarar Gwamna a zaben 2027

"Atiku yana da lafiya, ba shi da wata cuta a shekarun nan in ban da ciwo da ya ji a kafafunsa da yake mataimakin shugaban kasa."

- Adnan Mukhtar Tudunwada

An ce a LP da NNPP su bi Atiku a 2027

Idan zaben 2027 ya zo, kuna da labari Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya ce Atiku Abubakar ne mafita a kan sauran 'yan jam'iyyun adawa.

Matashin ‘dan adawan yana so jagororin Obidient da Kwankwasiyya su bi bayan jam’iyyar PDP domin gudun a raba kuri’u irin na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel