Labari Mai Daɗi: Malaman Makaranta Za Su Samu Ƙarin N35,000 a Albashi Duk Wata a Jihar APC
- Gwamnatin jihar Legas ta yi ƙarin haske kan alawus ɗin N35,000 na rage raɗaɗin halin da ake ciki ga malaman makaranta
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa malaman firamare zasu samu wannan tallafin daidai da yadda ake biyan sauran ma'aikata
- Sanwo-Olu ya ce malaman makarantun jihar Legas za su samu ƙarin N35,000 a matsayin tallafi kamar yadda ake biyan sauran ma'aikatan gwamnati
Jihar Legas - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, ya ba da umarnin a cire banbanci wajen biyan tallafin albashi na N35,000.
Gwamnan na jam'iyyar APC ya bada umarnin kada a sake nuna banbanci wajen biyan waɗannan kuɗin rage zafi ga malaman makarantun gwamnati a Legas.
![Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.](https://cdn.legit.ng/images/1120/7c5cebf482ba5e5b.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Idan baku manta ba a watan Disamba, 2023, gwamnan ya amince da biyan N35,000 ga duk ma'aikatan jihar.
Wannan ƙarin N35,000 a albashin ma'aikatan an yi shi ne domin rage musu raɗaɗin halin da aka shiga na tsadar rayuwa gabanin a ƙarkare batun sabon mafi ƙarancin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Vanguard ta tattaro, kwamishinan ilimi a matakin farko da na sakandire, Jamiu Alli-Balogun, ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki.
Ali-Bologun ya shaida wa kungiyar malamai (NUT) a ofishinsa cewa Gwamna Sanwo-Olu ya umarci a cire banbancin N20,000 da ake biyan malaman Firamare maimakon N35,000.
NUT ta yabawa Gwamna Sanwo-Olu
Shugabannin NUT karƙashin Kwamared Hassan Akintoye, sun yabawa gwamnan bisa wannan tagomashi da ya kara wa mambobin ƙungiyar.
Sun kuma bayyana cewa wannan matakin zai magance korafe-ƙorafen da malaman makaranta suke yi.
Akintoye, ya yabawa gwamnatin jihar Legas bisa ƙaunar da take yi wa malamai da kuma ci gaban ilimi.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/8283618869dcd174.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya gamu da cikas a CBN, wanda ya naɗa ya yi watsi da muƙamin kan dalili 1
Shugaban ya kuma jaddada goyon bayansa ga jihar baki daya tare da yin alkawarin "ci gaba da taimakawa gwamnati wajen cimma burinta na inganta koyo da koyarwa a jihar."
Tinubu ya soki ƴan kwadago
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya caccaki kungiyar kwadago ta ƙasa NLC kan zanga-zangar da ta yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa.
Shugaban ya ce ba zai yiwu NLC ta yaƙi gwamnatin da ba ta wuce wata 9 ba, yana mai cewa ba su ne kaɗai ke magana da muryar ƴan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng