Ganduje Ya Gamu da Matsala, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya da Dubban Mambobi Sun Koma PDP

Ganduje Ya Gamu da Matsala, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya da Dubban Mambobi Sun Koma PDP

  • Jam'iyyar APC ta rasa wasu manyan jiga-jiganta tare da dubban mambobi a jihar Oyo yayin da suka sauya sheƙa zuwa PDP ranar Alhamis
  • Shina Peller, tsohon mamban majalisar wakilan tarayya na ɗaya daga cikin waɗanda suka tattara suka koma PDP mai mulki a jihar
  • Fitaccen ɗan majalisar ya alaƙanta dalilinsa na sauya sheƙa zuwa PDP da kyakkyawan salon mulkin Gwamna Seyi Makinde

Jihar Oyo - A ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2024 jam'iyyar PDP mai mulki ta samu ƙaruwa ta manyan kusoshin siyasa a shiyyar Sanatan Oyo ta Arewa.

Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Shina Peller, tare da dubban mambobin Accord Party, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar People Democratic Party (PDP).

Shina Peller ya sauya sheka zuwa PDP.
Ganduje Ya Gamu da Naƙasu Yayin da Tsohon Dan Majalisa da Mambobin APC Suka koma PDP Hoto: Oyo State PDP News
Asali: Facebook

Meyasa Peller da dubban ƴan siyasar suka koma PDP?

Kamar yadda Punch ta rahoto, Gwamna Seyi Makinde, wanda mataimakin gwamna, Bayo Lawal ya wakilta, shi ne ya tarbi masu sauya sheƙar zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP zai ba 'yan adawa mukamai masu gwabi a jiharsa, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Peller ya samu nasarar lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Iseyin/Itesiwaju/Iwajowa/Kajola a majalisar wakilan tarayya a 2019 karkashin APC.

Sai dai a 2023 ya fice daga APC zuwa Accord Pary, inda ya tsaya takarar Sanatan Oyo ta Arewa amma ya sha ƙasa a hannun ɗan takarar PDP, Patai Buhari.

Tsohon ɗan majalisar ya ce kyakkyawan shugabanci na gari da Gwamna Seyi Makinde ke yi ne ya ja hankalisa zuwa PDP, cewar rahoton The Nation.

A kalamansa ya ce:

"Na ga ya dace na taho mu haɗa kai da Makinde. Babu shugabanci idan aka ce babu manufa kuma duk muna ganin dumbun ayyukan da Makinde ke zuba wa a shiyyar nan Oke-Ogun.
"Ba a taɓa ganin kamar haka ba a tarihin Oyo ta Arewa saboda haka idan kana da mutum mai manufa kamar Makinde, ya kamata ka goya masa baya, shiyasa na yanke zuwa na haɗu da Makinde mu ɗaga jihar Oyo."

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Jam'iyyar PDP ta tabbatar da ci gaban

A nasa ɓangaren, jam'iyyar PDP ta tabbatar da wannan ci gaban a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

PDP ta rubuta cewa:

"Hotunan sauya shekar Honorabul Shina Peller zuwa PDP a jihar Oyo wanda aka gudanar a Ojude-Oba, Iseyin."

Tinubu ya aike da saƙo ga Ɗangote da BUA

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya umarci kamfanonin da ke samar da siminti su koma asalin farashin siminti na baya kafin faɗuwar Naira.

Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Tinubu ya bai wa kamfanonin wannan umarni ne yayin ganawarsu a makon da ya wuce a Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel