Kano: An Bai Wa Abba Shawarar Yadda Zai Inganta Jihar Kamar Sanata Kwankwaso, Ya Yi Godiya

Kano: An Bai Wa Abba Shawarar Yadda Zai Inganta Jihar Kamar Sanata Kwankwaso, Ya Yi Godiya

  • Gwamna Abba Kabir ya samu muhimmiyar shawara daga gamayyar shugabannin jam’iyyar NNPP kan gudanar da mulki
  • Gamayyar ta shawarci gwamnan da ya kwaikwayi tsarin siyasa da mulki irin na tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso
  • Gamayyar shugabannin sun bayyana haka ne a yau Laraba 28 ga watan Faburairu inda suka ce hakan ne kadai zai ba da shugabnci mai nagarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gamayyar shugabannin jam’iyyar NNPP sun shawarci Gwamna Abba Kabir kan yadda zai gudanar da mulki.

Kungiyar ta bukaci gwamnan ya kwaikwayi mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kungiya ta shawarci Abba yadda zai inganta Kano kamar Kwankwaso
Gamayyar ta bai wa Abba shawarar ce don ganin ya inganta jihar Kano. Hoto: Rabiu Kwankwaso , Abba Kabir.
Asali: Twitter

Wace shawar suka bai wa Abba Kabir?

Gamayyar shugabannin NNPP sun bayyana haka ne a yau Laraba 28 ga watan Faburairu inda suka ce hakan ne kadai zai ba da shugabnci mai nagarta.

Kara karanta wannan

Kano: Duk da matakin kotu Abba zai dawo da rusau bayan sake daukar muhimmin mataki kan haka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma bukaci Abba Kabir kada ya gajiya wurin tabbatar da walwalar jama’ar jihar da kuma ayyukan more rayuwa, cewar Tribune.

Dakta Tosin Odeyemi wanda ya jagoranci tawagar ya bayyana haka ne yayin kai ziyara ofishin gwamnan a Kano.

Tawagar ta samu tarba daga mataimakin gwamnan jihar, Abdussalam Aminu Gwarzo da kwamishinoni da kuma wasu ‘yan Majalisar jihar.

Martanin Abba Kabir kan ziyarar

Gwarzo ya yabawa tawagar kan yadda suke damuwa kan ci gaban jihar Kano da kuma shawarwarin da suke bayarwa.

Tawagar ta tunatar da Abba cewa shekarar 2027 ta kusa inda ta shawarce shi da ya kara kaimi wurin ayyukan alkairi.

Yayin da suka bukaci Yusuf da kwaikwayi Kwankwaso, tawagar ta ce har yanzu Sanatan ya na da tasiri a siyasar jihar, cewar New Telegraph.

Suka ce duk da kasancewarsa tsohon gwamna amma tasirinsa ne ya ba su nasarar kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya kai ziyara ta musamman yankuna 2 da ƴan bindiga suka tafka ɓarna a jihar Arewa

An shawarci Kwankwaso kan siyasa

Kun ji cewa wani lauya mazaunin Kano ya shawarci Sanata Rabiu Kwankwaso yadda zai kafa kansa a siyasance.

Lauyan mai suna Umar Sa’ad Hassan ya ce Kwankwaso ya na da matukar tasiri a siyasar jihar da kuma mutunci.

Ya shawarci Kwankwaso yadda zai gina siyasarsa ta yi kamar yadda Buhari ya yi a Arewacin Najeriya ba tare da matsala ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel