Rigima Ta Ƙara Zafi a APC Yayin da Dakarun Ƴan Sanda Suka Kwace Iko da Sakateriya a Jihar Arewa

Rigima Ta Ƙara Zafi a APC Yayin da Dakarun Ƴan Sanda Suka Kwace Iko da Sakateriya a Jihar Arewa

  • Rikicin APC ya ɗauki sabon salo ranar Jumu'a yayin da aka wayi gari ƴan sanda sun kwace iko da sakateriyar jam'iyyar da ke Makurdi
  • A wata wasiƙa da kwamishinan ƴan sanda ya aike wa shugaban APC, ya ce sun hana dukkan wani taro da ya shafi siyasa a jihar
  • Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya bada umarnin dakatar da tarukan saboda yanayin taɓarbarewar tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar All Progress Congress (APC) reshen jihar Benuwai sun ɗauki sabon salo ranar Jumu'a, 1 ga watan Maris.

Rahoton Jaridar The Nation ya nuna cewa dakarun ƴan sanda na sashin yaƙi da masu tada tarzoma sun garzaya sun ƙwace iko da sakatariyar APC ta jiha.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta bada umarnin a ɗauki mutum 10 aikin ƴan sanda a kowace ƙaramar hukuma, ta faɗi dalili

Yan sanda sun kwace iko da sakateriyar APC.
Yan sanda sun hana taron SEC, sun kwace iko da sakateriyar APC a jihar Benue Hoto: Benue APC
Asali: Facebook

Tun da misalin karfe 7:00 na safiya aka ga jami'an ƴan sanda, jami'an rundunar Sibil difens da dakarun da ke kula da wuraren kiyo suka mamaye ƙofar shiga sakatariyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma jami'an tsaron sun yi cirko-cirko, sun toshe duk wata hanya da mutum zai bi ya shiga harabar sakateriyar APC.

Sun kuma yi amfani da motocinsu na aiki wajen toshe duk wani titi da zai sada mutum da sakateriyar APC mai mulki a jihar Benuwai.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka kan taron SEC?

Rundunar ‘yan sandan ta kuma dakatar da taron majalisar zartarwan jam'iyya ta jiha (SEC) da masu ruwa da tsakin APC da Comrade Austin Agada ke jagoranta wanda aka shirya yi yau.

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar APC, Kwamared Austin Agada, kwamishinan ‘yan sandan Benuwai, Emmanuel Adesina ya ce:

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

"Mun dakatar da taron majalisar zartarwa ta jiha da dukkan wasu tarukan siyasa har sai baba ta gani."

Wasiƙar na ɗauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ƴan sanda, (DCP) Samuel Gimba, da kuma adireshin Mista Agada.

Meyasa aka dakatar da taron SEC na APC?

Ya ce dakatar da wannan taro na SEC ya zama wajibi bisa umarnin Gwamna Hyacinth Alia na hana duk wani taron siyasa a faɗin jihar Benuwai.

A cewar ‘yan sanda, an yanke ɗaukar wannan matakin ne saboda tabarbarewar yanayin tsaro a Benuwai, rahoton AIT News.

Tsohon ɗan majalisar APC ya sauya sheƙa

A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC ta rasa wasu manyan jiga-jiganta tare da dubban mambobi a jihar Oyo yayin da suka sauya sheƙa zuwa PDP ranar Alhamis.

Shina Peller, tsohon mamban majalisar wakilan tarayya na ɗaya daga cikin waɗanda suka tattara suka koma PDP mai mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel