Rikicin APC Ya Kara Tsananta Yayin da Ƴan Sanda Suka Harba Barkono Kan Magoya Bayan Gwamnan Arewa

Rikicin APC Ya Kara Tsananta Yayin da Ƴan Sanda Suka Harba Barkono Kan Magoya Bayan Gwamnan Arewa

  • Yan sanda sun harba barkono mai sa hawaye kan dandazon masu ƙin jinin Austin Agada, shugaban APC na tsagin SGF Akume
  • Lamarin ya faro ne lokacin da Agada ya isa sakateriyar APC da ke Makurdi da nufin jagorantar taro, kwatsam magoya bayan gwamna suka tare shi
  • Gwamna Alia ya hana duk wani taron siyasa a jihar sabida yanayin taɓarɓarewar tsaro sakamakon kwararar miyagun makiyaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Alamu sun nuna kawo yanzu dai babu mai iya hango karshen rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar Progressives Congress (APC) ta jihar Benuwai.

Wannan na zuwa ne yayin da ƴan sanda suka harba barkonon tsohuwa mai sa hawaye kan tawagar masu zanga-zangar adawa da Autin Agada, shugaban APC na jihar.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Rikicin APC s jihar Benuwai.
Rikicin APC Ya Kara Tsanani a Benue Yayin da Yan Sanda Suka Tarwatsa Masu Zanga-Zanga Hoto: Benue APC
Asali: Facebook

A rahoton Channels tv, ƴan sanda sun harba masu barkonin ne yayin da tawagar ta yi yunƙurin faramakan Agada yayin da yake ƙoƙashin shiga sakateriyar APC da ke Makurɗi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Alia ya hana tarukan siyasa

Lamarin ya faru ne bayan shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar ya aike da saƙon umarnin Gwamna Hyacinth Alia ga kwamishinan ƴan sandan Benuwai, Emmanuel Adesina,

Gwamna Alia ya ba da umarnin hana duk wani taron siyasa sabida kwararar miyagun makiyaya wanda ya kara dagula sha'anin tsaron jihar Benuwai.

Bayan haka rundunar ‘yan sandan ta umurci APC karkashin jagorancin Agada da kada ta gudanar da taron kwamitin zartarwar jihar da ta shirya yi da wasu jiga-jigai.

Menene ya kawo harba tiyagas?

Duk da wannan umarnin, tawagar Agada da ake kyautata zaton suna biyayya ne ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, suka wuce kai tsaye domin yin taron.

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Kwatsam magoya bayan Gwamna Alia suka durfafi yankin kuma suka toshe titin da zai sada ka da wurin da su Agada suka tsara yin taronsu.

Amma tashin hankalin ya soma ne yayin da Mista Agada ya isa sakatariyar jam'iyyar APC, inda nan take masu zangar-zangar adawa da shi suka tare shi.

Hakan ne ya tilastawa jami'an yan sanda yin harbi a sama da harba barkonon tsohuwa kan mutanen domin tarwatsa su, Vanguard ta rahoto.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka a sakatariyar APC?

A wani rahoton kun ji cewa Rikicin APC ya ɗauki sabon salo ranar Jumu'a yayin da aka wayi gari ƴan sanda sun kwace iko da sakateriyar jam'iyyar da ke Makurdi.

A wata wasiƙa da kwamishinan ƴan sanda ya aike wa shugaban APC, ya ce sun hana dukkan wani taro da ya shafi siyasa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel