"A ƙara haƙuri" Abu 1 da Aka Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Yi Domin Magance Tsadar Rayuwa a Najeriya

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da Aka Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Yi Domin Magance Tsadar Rayuwa a Najeriya

  • Wani jigon jam'iyyar APC ya buƙaci ƴan Najeriya su kara haƙuri ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin nan gaba zasu ci moriyarsa
  • Anthony Adefuye ya kuma shawarci Tinubu ya gaggauta sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata domin kuɗi su wadata a hannun jama'a
  • Ya kuma nuna damuwa kan irin maƙudan kuɗin da ake kwatowa daga mutanen da suka yi aiki a karƙashin Gwamnatin Muhammadu Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Anthony Adefuye, mamba a majalisar ba da shawara kan harkokin mulki (GAC) a jam’iyyar APC reshen jihar Legas, ya bukaci ‘yan Nijeriya su ƙara hakuri da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Jigon jam'iyya mai mulkin ya kuma aminta da cewa ƴan Najeriya na fama da tsadar rayuwa da yunwa, amma a ganinsa ya kamata a kara ba Tinubu lokaci.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya keɓe minista 1, ya yaba masa kan yadda ya share hawayen ƴan Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Nemi Ƴan Najeriya Su Kara Hakura. Ya Faɗawa Tinubu Mafita Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Adefuye, sanatan Najeriya a jamhuriya ta uku, ya ce sauye-sauyen da shugaban ƙasa Tinubu ya ɓullo da su zasu zama alheri nan ba da daɗewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki ya dace Tinubu ya ɗauka?

Ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya sanar da mafi karancin albashi ga ma'aikata domin mutane su samu kudin siyan kayan amfani na yau da kullum maimakon jiran tallafi.

A wata hira da jaridar The Cable, Jigon ya ce:

“Ya zuwa yanzu, abubuwa sun fara kyau, Ina ganin ya kamata mu yi hakuri, kuna ganin yadda farashin dala ke saukowa yanzu. Na yi imani komai zai daidaita nan ba da jimawa ba.
"Abin da kawai nake so ya yi shi ne ya sanar da mafi karancin albashi da wuri-wuri domin mutane su samu damar siyan duk abin da suke so, maimakon tallafin da ake rabawa."

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Makudan kuɗin da ake kwato wa daga hadiman Buhari

Adefuye ya ce ya kaɗu matuka game da kudaden da aka kwato daga hannun wasu hadimai da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

"Wani abin damuwa a yanzu shi ne yadda ake kwato makudan kudade daga hannun wadanda suka yi aiki a gwamnatin Buhari.
"Ba wanda zai yi tunanin mutum mai tsauri da da’a kamar Buhari zai bari hakan ta faru a zamanin mulkinsa. Wannan shi ne kawai abin da ke damu na."

NLC ta jero dalilin yin zanga-zanga a Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa Ƴan kwadago sun bayyana cewa babban dalilin wannan zanga-zanga da mambobi suka fito shi ne yunwar da ƴan kasa ke ciki

Joe Ajaero ya ce batun mafi ƙarancin albashi abin dubawa ne amma ba shi ne asalin abinda ya haddasa NLC fara zanga-zangar kwana biyu ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel