Siyasar Najeriya
Jim kaɗan bayan sanatan LP ya koma APC, Hon Salman Idris na jam'iyyar ADC daga jihar Kogi ya sanar da bin sahunsa zuwa jam'iyya mai mulkin Najeriya ranar Talata.
Shugaban APC na rikon kwarya a jihar Rivers, Cif Tony Okochaya musanta raɗe raɗin da ke yawo cewa Nyesom Wike na da ta cewa a zartar da matakai a jam'iyyar.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Dele Momodu ya caccaki Bola Tinubu kan yiwa Najeriya kallon jihar Legas da zabo ministoci marasa kwarewa a mulkinsa.
Rahotanni da muka samu yanzu na nuni da cewa sanata mai wakiltar Imo ta Gabas kuma dan jam’iyyar Labour, Ezenwa Onyewuchi, ya koma jam’iyya mai mulki a kasa ta APC.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana da masu shirya zanga-zanda domin shawo kansu tun kafin dare ya yi.
Masu ruwa da tsakin APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara tuntuɓa da neman Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya tattaro kayansa ya baro jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar mai mulki a jihar Osun ta gamu da koma baya yayin da wasu mambobi sama da 100 suka jefar da laima, sun koma jam'iyyar APC ranar Lahadi, 21 ga wata.
Yayin da zaɓen jihar Edo ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta roki majalisar dokikin jihar ta gaggauta tsige Gwamna Obaseki kan kalaman da ya yi a bidiyo.
Jami'ai da ake zargin na farin kaya ne sun cafke wani Bashir Yunusa bayan ya tallata rigar zanga-zangar da ake shiryawa a Najeriya kan yunwa da matsin rayuwa.
Siyasar Najeriya
Samu kari