'Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Kudurin Neman Sauya Hanyar da Aka Bi Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

'Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Kudurin Neman Sauya Hanyar da Aka Bi Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

  • Ƙudirin da aka gabatar a gaban majalisar wakilai domin yin garambawul kan hanyar ayyana ƴan takarar da suka lashe zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni bai samu karɓuwa ba
  • Ƴan majalisar wakilan sun ƙi amincewa da ƙudirin bayan da aka gabatar da shi a zauren majalisar
  • Ƙudirin ko da majalisar ta amince da shi zai yi wahala ya zama doka saboda sai ya bi hanyoyi da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka da ke neman yin garambawul wajen ayyana ƴan takarar da suka lashe zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni.

Ƙudirin na neman tilastawa ƴan takarar shugaban ƙasa da na gwamna damar samun sama da kaso 50% cikin 100% na ƙuri’un da aka kaɗa, kafin a bayyana su matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓe, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Su wanene suka cancanci tallafin N25,000 duk wata na gwamnatin tarayya da yadda za a samu?

'Yan majalisa sun yi fatali da wani kudiri
'Yan majalisa sun yi fatali da kudirin neman yi wa kundin tsarin mulki garambawul Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Ƙudurin dokar wanda Awaji-inombek Abiante (PDP, Rivers) ya ɗauki nauyinsa, na da nufin yin gyara ga kundin tsarin mulki na 1999 ta hanyar kawar da hanyar da ake bi wajen ayyana waɗanda suka yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me sabon kuɗirin ya ƙunsa?

Ƙudirin na Mista Abiante na neman a gyara sashi na 134 da 179 na kundin tsarin mulki, wanda ya tanadi sharuɗɗan da za a bi wajen zaɓar shugaban ƙasa da gwamnoni, rahoton TheCable ya tabbatar.

Ƙudirin ya tanadi cewa idan aka samu ƴan takara sama da biyu a zaɓe, dole ne wanda ya yi nasara ya samu sama da kaso 50% cikin 100% na ƙuri’un da aka kaɗa.

Ƙudurin na da nufin hana abin da ya faru a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, inda Bola Tinubu, ɗan takarar APC mai mulki ya zama wanda ya yi nasara ba tare da samun rinjayen yawan ƙuri’un da aka kaɗa ba.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta yi kamu mafi girma a tarihinta, bayanai sun fito

Sai dai ƴan majalisar ba su yarda Mista Abiante ya jagoranci muhawara a kan ƙudirin ba.

Ƴan majalisa sun ƙi amincewa da ƙudirin

A lokacin da kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya gabatar da tambayar za a yi la’akari da ƙudirin dokar a karo na biyu, masu cewa “a’a” sun fi masu cewa “eh”.

Cikin kaɗuwa da faruwar lamarin, shugaban majalisar ya sake maimaitawa, inda muryoyin masu adawa da ƙudirin suka ƙara fin yawa.

Sakamakon haka sai kakakin majalisar ya amince da bukatar ƴan majalisar da ke son a yi fatali da ƙudirin.

To sai dai kuma ko da majalisar wakilai ta amince da kudirin, zai buƙaci ɗaukar dogon lokaci domin yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima.

Ƙudirin sai ya buƙaci amincewar majalisar dattawa da kuma amincewar majalisar dokoki ta jihohi 24 daga cikin 36 na Najeriya.

Majalisa Ta Kwafa Kwamitin Binciken Bashin da Buhari Ya Ƙarɓo

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki bashin N30trn da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓo.

Kwamitin zai binciki yadda aka kashe kuɗaɗen waɗana aka ciwo bashinsu daga babban bankin Najeriya (CBN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel