Jerin Manyan ’Yan Siyasa 5 da Wasu Jiga-Jigai da Suka Koma APC Bayan Hawan Tinubu Mulki

Jerin Manyan ’Yan Siyasa 5 da Wasu Jiga-Jigai da Suka Koma APC Bayan Hawan Tinubu Mulki

Siyasar Najeriya ta na zuwa da bazata musamman lokacin zabe ko bayan zabe ganin yadda manyan ‘yan siyasa ke sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata saboda wasu dalilai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Tun bayan hawan Shugaba Tinubu karagar mulki, akwai manyan ‘yan siyasa da suka watsar da jam’iyyunsu don komawa jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Mafi yawan masu sauya shekar sun gudu ne saboda ba su samu abin da suke nema daga jam’iyyar tasu ba.

Manyan 'yan siyasa da suka sauya sheka zuwa APC bayan hawansa kujerar mulki
Jam'iyyar APC ta karbi wasu jiga-jigai da suka watsar da jam'iyyarsu zuwa gareta. Hoto: Ramalan Yero, Salihu Yakasai, Rufa'i Alkali.
Asali: Facebook

Legit Hausa ta jero muku manyan ‘yan siyasar da suka sauya sheka zuwa APC bayan rantsar da Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

'Dan gida ya fasa kwai, ya jefi Gwamnatin Tinubu da biyewa manufofin turawa

1. Ramalan Yero

Tsohon gwamnan Kaduna, Yero ya sauya shekar ce watanni biya bayan watsar da jam’iyyar PDP.

Yero ya mulki jihar Kaduna daga shekarar 2012 zuwa 2015 a PDP kafin sauya sheka zuwa APC a ranar 11 ga watan Faburairun 2024.

2. Farfesa Ahmed Rufa’i Alkali

Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP ya bai wa kowa mamaki bayan komawa APC da wasu ‘yan jam’iyyar masu yawa.

Rufa’i ya sauya shekar ce a ranar 30 ga watan Oktobar 2023 da wasu jiga-jigan jam’iyyarsa ta NNPP, cewar Daily Trust.

3. Sanata Ifeanyi Uba

Uba wanda ke wakiltar Anambra ta Kudu ya koma jam’iyyar APC a watan Oktobar 2023 daga jam’iyyar YPP.

Daga bisani ya samu tarba mai kyau da shi da kuma manyan shugabannin jam’iyyar daga jihar a ofishin shugaban APC, Umar Ganduje.

4. Salihu Tanko Yakasai

Yakasai tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PRP a Kano ya koma APC a ranar 30 ga watan Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Gamu da Matsala, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya da Dubban Mambobi Sun Koma PDP

Salhu ya bayyana sauya shekar ta shi ne bayan kai ziyara sakatariyar jam'iyyar inda ya ce Ganduje ne ya bukace shi ya dawo jam’iyyar don kara inganta ta, cewar TheCable.

5. Halliru Dauda Jika

Jika shi ne tsohon dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar NNPP a zaben da aka gudanar a shekarar 2023.

Bayan komawa APC, Halliru ya bukaci mambobin jam’iyyar a jihar su hada kai don shirin zaben 2027 a jihar baki daya.

Sauran manyan ‘yan siyasa da suka koma APC akwai ‘yan takarar gwamna a jihohin Kaduna da Benue da Yobe da sauran manyan ‘yan siyasa.

‘Yan Majalisu 27 a Rivers sun koma APC

Kun ji cewa ‘yan Majalisun jihar Rivers akalla 27 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC inda suka birkita gwamnan jihar.

Wannan sauya sheka na zuwa ne yayin da aka ci gaba da rikici tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel