Shugaba Tinubu Ya Keɓe Minista 1, Ya Yaba Masa Kan Yadda Ya Share Hawayen Ƴan Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Keɓe Minista 1, Ya Yaba Masa Kan Yadda Ya Share Hawayen Ƴan Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya keɓance ministan harkokin cikin gida, ya yaba masa bisa sauye-sauyen da ya kawo wanda ya rage fushin ƴan Najeriya
  • Shugaban ƙasar ya ce ya ji da kunnensa yadda Tunji-Ojo ke shan yabo daga ƴan Najeriya, inda ya ce hakan ya fara ɗaga martabar ƙasar nan
  • Tun da ya shiga ofis a matsayin ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya warware matsalolin farfo 20,000 da aka riƙe kafin zuwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, bisa sauye-sauye masu amfani da ya bullo da su a ƙasar nan.

Bola Tinubu ya jinjinawa ministan ne a wurin taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) wanda aka gudanar ranar Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tsohon gwamna ya nemo mafita ga 'yan Najeriya

Bola Tinubu da ministan cikin gida, Tunji Ojo.
Shugaba Tinubu Ya Yabawa Ministan Cikin Gida Bisa Sauye-Sauyen da Ya Kawo Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa an samu sauƙin koken ƴan Najeriya sosai duk a sakamakon dabarun da Tunji-Ojo ya bullo da su a ma'aikatar cikin gida, Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi na musamman kan ministan cikin gida shi kaɗai, Tinubu ya ce ya samu bayanai masu kyau daga bakunan ƴan ƙasa kan gyaran da Olubunmi Tunji-Ojo ya ɗauko yi.

A cewarsa, aikin da ministan ke yi ya fara farfaɗo da ƙimar ƙasar nan da kuma rage fushi da kukan ƴan Najeriya game da wasu tsare-tsaren gwamnatin Najeriya.

Wane sauye-sauye ministan ya ɓullo da su?

Tun bayan lokacin da Olubunmi Tunji-Ojo ya shiga ofis a matsayin ministan harkokin cikin gida, cikin makonni biyu ya warware fasfo 20,000 da suka maƙale.

Ministan ya cimma wannan nasara ba tare da ya jawo wa gwamnatin tarayya ƙarin kashe-kashen kuɗi ba.

Kara karanta wannan

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da aka buƙaci Shugaba Tinubu ya yi domin magance tsadar rayuwa a Najeriya

Ya kuma kafa yadda kowa zai iya neman fasfo kai tsaye, lamarin da ke shan yabo daga bakunan ƴan Najeriya a ciki da wajen ƙasar nan, rahoton The Nation.

Har ila yau, a karkashinsa, ma'aikatar harkokin cikin gida za ta kaddamar da aikin kafa E-Gates a duk fadin filayen jiragen sama na kasa da kasa a Najeriya.

Tinubu ya nufi jihar Ondo

A wani rahoton kun ji cewa Ahmed Tinubu ya kama hanyar zuwa Ondo domin yin ta'aziyyar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, wanda aka ɓinne shi ranar Jumu'a

Rahoto ya nuna cewa bayan ta'aziyya ga iyalansa, shugaban ƙasar zai ziyarci Sarkin Owo da kuma shugaban kungiyar yarbawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262