Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun farmaki shingen bincike a yankin mahaifar mai girma gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Soludo.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Miyagun sun hallaka mutane takwas a harin da suka kai a cikin dare.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace basarakena jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, ƴan sanda sun fara farautarsu domin ceto shi.
An samu barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu kauyukan jihar Taraba. Rikcin ya jawo an samu asarar rayukan mutane daga bangaren manoma da makiyaya.
Gwamnan jihar Zamfara ya tabo batun matsalar rashin tsaron sa ake fama da ita. Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta hawa teburin sulhu da 'yan bindiga.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da sake kama wanda ake zargi da hannu a kisan ɗan Majalisar Dokokin jihar Anambra, Justice Azuka bayan ya tsere a baya.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu fusatattun matasa a garin Tsiga da ke jihar Katsina sun kone fadar dagacin garin bayan wani barawo ya nemi mafaka.
'Yan sanda sun karyata cewa jirginsu ya kai wa 'yan bindiga kaya a Kogi. Sun ce aikin tsaro ne suka gudanar tare da 'yan banga da wasu jami'an tsaro a jihar.
Bayan yada bidiyon jirgi da ake zargin yana sauke makamai ga yan bindiga, rundunar 'yan sanda ta musanta rade-radin kai kayan abinci ga 'yan ta'adda a jihar Kogi.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari