Malamin Addini Ya Rikita Al'umma da ya Kashe Yara 4 Ƴan Gida Ɗaya da Taɓarya
- Wani fasto a Ibagwa-Aka, Igbo-Eze ta Kudu, Enugu, ya halaka yara hudu da tabarya lamarin ya girgiza al’umma tare da tayar da hankula
- Shugaban karamar hukumar, Ferdinand Ukwueze, ya ziyarci iyalan mamatan, ya ce gwamnati za ta tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu
- Iyayen yaran sun nemi a yi bincike sosai bayan kama wasu da ake zargi, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da farautar sauran da suka tsere
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - An shiga wani irin yanayi a jihar Enugu bayan wani Fasto ya yi aika-aika na kisan kai wurin amfani da tabarya.
A cikin garin Ibagwa-Aka da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu a Enugu, mummunan lamarin ya girgiza iyali da daukacin al’umma.

Asali: Original
Fasto ya hallaka yara 4 a Enugu
Faston ya hallaka yara hudu ‘yan uwan juna, Kamsiyochukwu Ezema (7), Ezinne Ezema (6), Ujunwa Ezema (5), da Chinedu Ezema (2) aka kashe da tabarya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faston da ke cocin sabbath a yankin ne ake zargin ya aikata wannan kisan, kuma har yanzu ba a san dalilin hakan ba.
Shugaban karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu, Mista Ferdinand Ukwueze, ya nuna bakin ciki da fushi, ya ce dole a hukunta shi idan aka gama bincike.
Ya ce:
“Al’ummarmu ta girgiza da kisan gilla da aka yi wa yaran nan guda hudu a Ibagwa-Aka."
Ukwueze ya kai ziyara wajen da abin ya faru tare da ‘yan sanda, DSS da jami’an tsaro domin duba lamarin da daukar matakin gaggawa.
“Binciken farko ya sa aka kama wasu masu hannu a kisan yayin da aka ci gaba da neman wasu da ke gudun hijira."
- A cewar Ukwueze

Asali: Facebook
Hukumomi sun yi alkawarin hukunta Fasto
Ukwueze ya ba da umarnin a kulle wajen da aka aikata kisan, wanda ake amfani da shi don maganin gargajiya da ayyukan tsafi.
Ya kara da cewa:
“Za mu ci gaba da tallafa wa bincike har sai an hukunta wadanda ke da hannu."
Iyayen yaran, Chinonso Ezema da Loveth Ezema, sun nemi a yi adalci.
Mahaifin ya ce:
“Muna so ‘yan sanda su bincika sosai kuma a hukunta kowa."
Yayin da al’umma ke jimamin rasuwar yaran, hukumomi na kokarin ganin an hukunta masu laifi tare da kare afkuwar irin haka a gaba.
Ana kokarin tuntubar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Enugu, SP Daniel Ndukwe, amma bai amsa kiran waya da sakon tes ba.
Matashi ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
Mun ba ku labarin cewa ana zargin wani matashi, Safiyanu Dalhatu ya hallaka mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi, lamarin da ya jefa al’umma a firgici da jimami.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wanda ake zargi tare da kwace tabaryar da ya yi amfani da ita wajen aikata wannan aika-aika.
Binciken farko na 'yan sandan ya nuna rikici tsakanin Safiyanu da mahaifiyarsa ne ya harzuka matashin har ya farmaki gyatumarsa.
Asali: Legit.ng