Asirin Wanda Ake Zargi da Hannu a Kashe Ɗan Majalisa Ya Tonu, Yan Sanda Sun Cafke Shi

Asirin Wanda Ake Zargi da Hannu a Kashe Ɗan Majalisa Ya Tonu, Yan Sanda Sun Cafke Shi

  • Ƴan sanda sun yi nasarar sake cafke wanda ake zargi da hannu a kisan ɗan Majalisar Dokokin jihar Anambra, Justice Azuka
  • Mahara sun sace Hon. Azuka ranar 24 ga watan Disamba, 2024, kuma bayan wasu makonni jami'an tsaro suka gano gawarsa
  • A binciken da ake yi kan wannan aikata-aikata, ƴan sanda sun kama Ikemefuna Ossai bisa zargin da hannunsa a kisan amma ya tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Rundunar 'yan sanda a Jihar Anambra ta tabbatar da sake kama wanda ake zargi da hannu a garkuwa da kuma kisan gilla da aka yi wa marigayi Hon. Justice Azuka.

Mutumin da ake zargin yana da hannu a kisan ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Onitsha 1 a Majalisar Dokokin Jihar Anambra ya tsere ne bayan an kama shi a baya.

Justice Azuka.
Yan sanda sun sake kama wanda ake zargi da kisan dan majalisa a Anambra Hoto: Nigeria Police Force, Hon. Justice Azuka
Asali: Facebook

Kakakin rundunar, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da sake cafke wanda ake zsrgin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Onitsha, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kama wanda ake zargin, Ikemefuna Ossai, a ranar 7 ga Mayu, bayan dogon bincike da bin diddiginsa a jihohi da dama da ma wasu kasashen makwabta.

Yadda aka kashe ɗan Majalisa a Anambra

Idan ba ku manta ba marigayi Azuka ya fada hannun masu garkuwa da mutane ne a ranar 24 ga Disamba, 2024, a hanyar Ugwunapampa, Onitsha, yayin da yake dawowa gida.

Bayan makonni da dama, hukumomin tsaro suka gano gawarsa a gadar Neja ta biyu a ranar 6 ga Fabrairu, 2025.

Kakakin ƴan sanda ya ce wanda ake zargin da ya taba tserewa a baya, ya yi yunkurin tserewa lokacin da aka je kama shi a Asaba, Jihar Delta, amma jami'ai suka harbe shi a ƙafa.

Asirin wanda ake zargi ya tonu

Ya ce rundunar ƴan sanda ta riga ta sanar da iyalan marigayin da kuma shugabannin majalisar dokokin jihar Anambra dangane da wannan ci gaban.

Kwamishinan ‘yan sandan Anambra ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka bari wanda ake zargin ya tsere a baya, rahoton Leadership.

Yan sanda.
Yan sanda sun ce duk mai hannu a kisan ɗan Majalisa zai girbi abin da ya shuka Hoto: Nigeria Police Force
Asali: UGC

Kwamishinan ya ce:

"Wannan nasarar da aka samu za ta taimakawa bincike da kuma kokarin gano sauran waɗanda ke da hannu a wannan aika-aikar.
"Rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da kokarin ganin an kamo duk wadanda ke da hannu a wannan kisa tare da tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.”

Rundunar ta kuma nanata kudirinta na ganin an gurfanar da duk masu hannu a lamarin kisan Hon. Azuka gaban kuliya domin girbar abinda suka shuka.

'Yan sanda sun karyata kai wa miyagu makamai

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa jirgin sama ya kai kayan abinci ko makamai ga 'yan bindiga a jihar Kogi

Jama'a sun yi ta yada wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta, suna zargin jirgi mai saukar ungulu na raba makamai ga yan bindiga a wani daji.

Ƴan snada sun musanta zargin da cewa jirgin yana taimakawa jami'an tsaron haɗin guiwa ne wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci a Kogi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262