Mummunan Hatsarin Mota Ya Lamushe Rayukan Iyalan Tsohon Kwamishina 'Baki Ɗaya'
- Iyalan wani tsohon Kwamishina a Niger sun mutu bayan gamuwa da mummunan hatsarin mota wanda ya yi ajalinsu
- Hatsarin ya rutsa da fasinjoji 18 a hanyar Kutigi zuwa Bida, inda mutane tara suka mutu, bakwai suka samu raunuka, hudu kuma ba su ji rauni ba
- ’Yar Daja daya ce ta tsira daga motar Mazda, amma ta samu munanan raunuka da suka hada da karyewar hakarkari da kafada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Matar tsohon Kwamishinan Ilimi na Niger, Abubakar Daja, da ’ya’yansa uku sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru ranar Lahadi.
Hatsarin ya hada wata mota kirar Sienna da Mazda, inda matar marigayin da ’ya’yanta hudu suke tafiya daga Minna zuwa hanyar Mokwa-Bida.

Source: Original
Abubakar Daja, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Mashegu, ya rasu a shekarar 2025, ya rike matsayin Kwamishinan Ilimi bayan komawar mulkin dimokuradiyya, cewar Punch.
Daja ya zama kwamishinan ne a shekarar 1999, kuma ya yi wa’adin mulki biyu kafin ya kammala aiki a shekarar 2007.
Yadda iyalan tsohon kwamishinan suka mutu
Rahotanni sun bayyana cewa marigayiya Hajia Daja da ’ya’yanta hudu suna cikin motar Mazda yayin da hatsarin ya afku a hanyar.
Matar da ’ya’yanta uku sun mutu nan take, yayin da ’yarta daya tilo da ta tsira ta samu munanan raunuka a hatsarin.
An ce yarinyar, wadda ba ta kai shekarun girma ba, ta samu karyewar hakarkari da kafada, kuma tana cikin mawuyacin hali bayan hatsarin.
Wani ganau daga Karamar Hukumar Mokwa, Salihu Abubakar, ya ce bai da tabbacin ko yarinyar za ta tsira saboda tsananin raunukan da ta samu.

Source: Twitter
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu
Majiyoyi sun gano cewa mutane biyu da ke cikin motar Sienna su ma sun mutu, lamarin da ya kai adadin wadanda suka rasu zuwa tara.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Saadu, wadda ta tabbatar da hatsarin mota a daren Lahadi, ta ce mutane 18 ne suka shiga cikin hatsarin, yayin da bakwai suka samu raunuka.
Ta bayyana cewa bakwai sun mutu, hudu kuma ba su samu wani rauni ba. Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Lahadi.
A cewar Saadu, hatsarin ya faru ne a kauyen Shebe da ke kan hanyar Kutigi zuwa Bida, inda motoci biyu suka yi karo tare da jikkata mutane da dama.
Bayanan da aka fi mayar da hankali a labarin: mutane tara ne suka mutu, bakwai suka ji rauni, yayin da hudu suka tsira ba tare da wani rauni ba, cewar Daily Post.
Mataimakin gwamna ya gamu da hatsarin mota
Mun ba ku labarin cewa Motocin ayarin mataimakin gwamnan jihar Cross River, Peter Odey, sun gamu da hatsari a kan hanyar Ikom zuwa Kalaba.
Hatsarin ya faru ne kusa da Ugep da ke a karamar hukumar Yakurr, kuma mutane da dama daga cikin hadimansa sun ji raunuka.
Rahotanni sun nuna cewa mataimakin gwamnan ya tsallake rijiya da baya, amma wasu daga cikin motocin ayarin sun lalace.
Asali: Legit.ng
