Gwajin DNA Ya Yi Tonon Silili, Kashi 23 na Yaran Najeriya ba na Iyayensu Maza ba ne

Gwajin DNA Ya Yi Tonon Silili, Kashi 23 na Yaran Najeriya ba na Iyayensu Maza ba ne

  • Wani rahoto ya nuna cewa kashi 23.6 cikin 100 na gwaje-gwajen DNA da aka gudanar a Najeriya ya ballo ruwa game da aininhin iyayen yaran
  • Rahotanni sun bayyana cewa gwaje-gwajen sun tabbatar da cewa yaran ba ’ya’yan mazajen da ake zaton su ne iyayensu ba
  • Binciken Smart DNA ya nuna cewa kusan mutum ɗaya cikin huɗu daga cikin waɗanda aka yi wa gwajin bai kasance mahaifin 'dan aka lakaya masa ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria – Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kashi 23.6 cikin 100 na gwaje-gwajen DNA da aka gudanar a Najeriya domin tantance mahaifin yaro sun jawo cece-kuce.

Binciken da aka rika yi sun nuna cewa mutanen da ake zaton su ne iyayen yaran ba su ne ainihin mahaifansu ba kamar yadda aka rika tsammani.

Kara karanta wannan

Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu

Gwajin DNA ya gano shegu a Najeriya
Hannun uwa rike da jaririnta (Wannan hoto an yi amfani da shi ne don misali) Hoto: Getty
Source: Getty Images

DW ta wallafa cewa kungiyar Smart DNA ce ta gudanar da binciken a tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026. Sakamakon ya nuna cewa kusan mutum ɗaya cikin huɗu daga cikin mutanen da aka yi wa gwajin ba uban dansa ba ne.

Gwajin DNA ya yi bankada

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Wannan adadi ya yi ƙasa kaɗan idan aka kwatanta da kashi 24 cikin 100 da aka samu a wasu rahotannin baya.

A cewar Smart DNA, sakamakon binciken ya nuna muhimmancin gwajin tantance uba wajen taimaka wa iyalai su gano gaskiyar asalin yara tare da magance shakku da ka iya tasowa tsakanin ma’aurata.

Ƙungiyar ta ce mutane da dama da ke zuwa domin yin gwajin ba wai wani ne ya tilasta musu yin hakan ba. Maimakon haka, suna neman amsa ne saboda sun kasa ci gaba da rayuwa cikin rashin tabbas.

Jama'a na rungumar gwajin DNA

Kara karanta wannan

Amaechi: Mataimakin Atiku ya bukaci 'yan Najeriya kada su zabi ADC, an ji dalili

Bayanan da aka samu daga ɗakunan gwaje-gwajen sun kuma nuna cewa gwajin DNA ya zama wata hanya mai muhimmanci da iyalai ke amfani da ita wajen warware wasu tambayoyi masu tsauri.

An gano kashi 23 na yaran Najeriya ba na iyayensu maza ba ne
Ana rungumar DNA a tsakanin iyaye a yanzu Hoto: Choochiin
Source: Getty Images

Elizabeth Digia daga Smart DNA ta ce:

"Yawancin maza da mata da suke zuwa wurinmu ba wai don wani ya gaya musu su zo ba ne, suna zuwa ne saboda ba za su iya rayuwa da wannan tambayar a zuciyarsu ba."

Rahoton ya ƙara jaddada muhimmancin sanin asalin yaro, musamman a yanayin da ake fama da shakku ko rashin fahimtar juna.

Kasar da ake ba da tallafin haihuwa

A baya, mun kawo labarin cewa Gwamnatin Singapore ta sanar da sabon tsarin tallafi da zai bai wa kowane yaro da ya cancanta tallafin gwamnati da ya kai kwatankwacin N94m.

Firaministan Singapore, Lawrence Wong, ya ce sabon tsarin zai saukaka hanyoyin tallafa wa iyalai tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu tallafin domin inganta rayuwarsa.

An ce shirin zai amfani sama da yara 610,000 daga gidaje kusan 380,000, domin karfafa gwiwar iyalai su kara haihuwa yayin da ake fuskantar raguwar haihuwa a tsakanin ma'auratan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng