An Gano Adadin Mutanen da Yan Bindiga Suka Hallaka a Harin Masallatan Neja
- An kashe akalla mutum 30 daga cikin masallatan da aka sace yayin sallar Juma’a a wasu masallatai hudu a karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja
- ‘Yan bindiga sun kai hare-haren ne lokaci guda a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, inda suka tafi da sama da mutum 60 zuwa daji
- Hare-haren sun tilasta daruruwan mazauna yankin tserewa zuwa New Bussa da Jamhuriyar Benin, yayin da aka rufe wasu kasuwanni saboda tabarbarewar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Niger – Akalla mutum 30 ne aka kashe bayan wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare kan masallatai hudu a karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja a ranar Juma’a 21 ga watan Agusta, 2026.
‘Yan bindigan sun kai hare-haren ne a lokaci guda yayin da ake gudanar da sallar Juma’a a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, inda suka yi awon gaba da daruruwan masu ibada.

Source: Facebook
Jaridar Punch da ta ruwaito harin ta ce maharan sun tattara masu ibadar bayan sun shiga masallatan, sannan suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Adadin mutanen da aka kashe a Neja
Da yake magana da Daily Trust ranar Litinin 2 ga watan Agusta, 2026, shugaban karamar hukumar Borgu, Mohammed Nasir Abdullahi, ya tabbatar da cewa kusan mutum 30 daga cikin wadanda aka sace sun mutu a hannun masu garkuwar.
Ya ce al’ummomin yankin sun gano gawarwakin wadanda aka kashe tare da birne su ba tare da sanin makusantansu ba bayan hare-haren.
Shugaban ya ce:
“Sojoji sun shiga can. Yanzu komai ya lafa. Mun rasa wasu mutane, kuma an yi jana’izarsu. Wasu mutane sun gudu zuwa wuraren da suka fi aminci.
“Bisa bayanan da nake da su, wadanda aka sace sun dan haura 60. Wadanda aka kashe sun kusa 30."
Yadda yan bindiga suka yi ta'asa
Mohammed Yasir Abdullahi ya kara da cewa an kona wasu gidaje a lokacin harin, ciki har da gidan shugaban gundumar Dekara, Abubakar Umar.ssss

Source: Original
Shugaban karamar hukumar ya ce an sace mutanen ne daga garuruwa hudu yayin da suke gudanar da sallar Juma’a a makon da ya gabata.
Bayan hare-haren na ranar Juma’a, daruruwan mazauna yankin sun tsere zuwa New Bussa da Jamhuriyar Benin bayan ‘yan ta’addan sun yi barazanar kashe duk wanda ya ci gaba da zama a yankunan da abin ya shafa.
Gwamnan Neja ya dauki zafi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da cewa yan bindiga sun sace masulmai yayin sallar Juma’a a yankin karamar hukumar Borgu Gwamna Mohammed Umaru Bago ya umurci jami’an tsaro su dauki matakan ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin gaggawa Gwamnati ta gargadi jama’a kan yada bayanan da ba a tabbatar da su ba kan lamarin harin da yan bindigar suka kai Read more: https
Asali: Legit.ng

