Dambarwa: Mata Ta Gutsure Mazakutar Masoyinta yayin Rigimar Saduwa

Dambarwa: Mata Ta Gutsure Mazakutar Masoyinta yayin Rigimar Saduwa

  • Rundunar ‘yan sanda a Jihar Rivers ta kama wata mata mai suna Gift bayan ta yanke mazakutar saurayinta a unguwar Diobu a Port Harcourt
  • Rikicin ya samo asali ne bayan saurayin, Sunday, ya nemi saduwa da ita amma Gift ta ƙi saboda wai yana amfani da maganin ƙara ƙarfin maza
  • Daga bisani, Sunday ya kai mata hari, sai ta kama al’aurarsa da baki ta gutsure, kafin ‘yan sanda su zo su shiga lamarin bayan rahoton da suka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Rivers ta kama wata mata da zargin gutsure mazakutar masoyinta yayin arangama kan mu'amalar aure.

An cafke matar mai shekara 43 mai suna Gift bisa zargin aikata hakan ne yayin rigima da saurayinta a Diobu da ke Rivers a Kudancin Najeriya.

Mata ta gutsure mazakutar saurayinta
Mata ta yanke mazakutar saurayinta a Rivers. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mata ta gutsure mazakutar saurayinta a Rivers

Punch ta ce lamarin da ya faru ranar Alhamis 15 ga watan Mayun 2025 ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye a unguwar da ke cike da jama’a a Port Harcourt.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasu majiyoyi, hatsaniyar ta fara ne bayan saurayin Gift mai suna Sunday ya nemi su sadu da juna.

Gift ta ƙi amincewa da hakan, inda ta zarge shi da cewa yana amfani da magungunan ƙara ƙarfin maza wanda ke janyo tsawaitar saduwa.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Mista Sunday ya fusata, sai ya yi kokarin afka mata ta ƙarfi saboda kin amincewar da ta yi.
“A lokacin artabu, Gift ta kama mazakutar saurayin da bakinta, ta gutsure kayin gaba ɗaya."
An kama mata da ta gutsure mazakutar saurayinta
Mata ta yanke mazakutar saurayinta a Rivers. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

An ce ihu da kukan saurayin ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda wasu suka yi yunkurin kai farmaki kan matar kafin ‘yan sanda su iso.

Jami’an ‘yan sanda daga ofishin Nkpolu tare da DPO sun kawo ɗauki, suka ceto ta sannan suka kama ta, cewar The Sun.

An garzaya da Sunday zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin a ba shi agajin gaggawa a kokarin ceto rayuwarsa daga mummunan yanayin da ya shiga.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Eh, na tabbatar da lamarin, an kama matar (wacce ake zargi) mai shekara 43, ana ci gaba da bincike domin gano bakin zaren da kuma matakin da za a ɗauka a gaba."

- Cewar Iringe-Koko.

Amarya ta datse mazakutar mijinta a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa an shiga tashin hankali a garin Kudan da ke jihar Kaduna, bayan wata amarya ta yanke mazakutar angonta yana barci a gado.

An ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Mayun 2024 yayin da aka wuce da angon mai suna Salisu Idris asibiti domin jinyar raunin.

Salisu ya bayyana kaduwarsa kan aika-aikar da amaryarsa Habiba Ibrahim ta yi masa duk da babu wani sabani a tsakaninsu kafin faruwar hakan a tsawon zaman da suka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.