Atiku Ya Sake Haduwa da Fushin Gwamnatin Tinubu kan Maido Tallafin Mai

Atiku Ya Sake Haduwa da Fushin Gwamnatin Tinubu kan Maido Tallafin Mai

  • Gwamnatin tarayya ta ce sake dawo da tallafin man fetur zai iya jefa Najeriya cikin matsalar tattalin arziki tare da rusa wasu nasarorin da aka samu
  • Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce cire tallafin ya samar wa tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi karin kuɗi
  • Gwamnatin ta bayyana cewa maido da tallafin zai iya kawo sabon cikas ga masu zuba jari da kuma ci gaban matatun mai na cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk wani yunkurin sake dawo da tallafin man fetur zai iya rusa nasarorin da Najeriya ta samu a bangaren tattalin arziki tun bayan cire tallafin a shekarar 2023.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a wani bayani, yana mai cewa ya kamata a yi nazari mai zurfi kan irin matsalolin da tsohon tsarin tallafin ya jawo wa tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Mohammed Idris a wajen taro
Ministan yada labarai, Mohammed Idris. Hoto: Federal Ministry of Information
Source: Facebook

Punch ta rahoto ya ce tsarin tallafin man fetur ya kasance babban nauyi ga gwamnati, inda Najeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin mai a shekarar 2022.

Nasarorin cire tallafin mai

Mohammed Idris ya ce bayan cire tallafin man fetur, gwamnati ta samu karin damar tattara kuɗi da kuma bai wa matakai daban-daban na gwamnati damar gudanar da ayyukan ci gaba.

A cewarsa, bayanan gwamnatin tarayya sun nuna cewa cire tallafin ya samar da Naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

Ya ce daga cikin kuɗin, gwamnatin tarayya ta samu kusan N5.43tn, jihohi suka samu N6.52tn, yayin da ƙananan hukumomi suka samu N3.88tn.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a wajen taron APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Business Day ta wallafa cewa bayanan gwamnati sun nuna cewa an kashe kusan N6.47tn wajen wasu muhimman ayyukan abubuwan more rayuwa.

Dalilin kin maido tallafin mai

Mohammed Idris ya ce sake dawo da tallafin man fetur zai iya kawo cikas ga ci gaban da Najeriya ke samu wajen bunkasa matatun mai na cikin gida.

Kara karanta wannan

Jigo a APC kuma dan kasuwar mai ya kwancewa Atiku zani kan dawo da tallafin fetur

Ya ce Najeriya na kara samun damar tace man fetur a cikin gida, lamarin da zai iya taimakawa wajen inganta samar da mai da kuma karfafa tsaron makamashi.

A cewarsa, sauya tsarin gwamnati a yanzu na iya haifar da rashin tabbas ga masu zuba jari, musamman a lokacin da ake kokarin karfafa masana'antar tace mai ta cikin gida.

Kenneth Okonkwo ya kare Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa kakakin yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya yi watsi da sukar maido tallafin man fetur.

Okonkwo ya ce manufar Atiku ba wai dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur ba ne, illa samar da wani tsari da zai rage tsadar tace mai tare da bai wa 'yan Najeriya damar samun fetur cikin sauki.

Ya ce Atiku ya yi imanin cewa amfani da matatun mai na cikin gida da sauran sauye-sauye za su iya taimakawa wajen rage farashin fetur da kuma inganta karfin sayen kayan masarufi na 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng