'Yan Bindiga Sun Shammaci Jami'an Tsaro a Wani Hari, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Shammaci Jami'an Tsaro a Wani Hari, an Samu Asarar Rayuka

  • Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu a harin da suka kai Tanjol da Tarai a gundumar Jol, Riyom, jihar Plateau
  • Maharan sun kwace bindigogin jami’an da aka kashe, yayin da wasu mutane suka jikkata kuma aka rawaito cewa wani farar hula ya bace
  • Harin ya ƙara tayar da fargaba a Riyom, inda aka samu wasu hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro a makonnin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - An kashe jami’an tsaro biyu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyukan Tanjol da Tarai da ke gundumar Jol, Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Plateau a ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi musayar wuta da jami’an tsaro

An ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana, inda maharan suka yi arangama da jami’an tsaro da suka mayar da martani, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

Mazauna yankin sun shaida cewa jami’an tsaron sun isa wurin bayan samun labarin harin, amma suka gamu da turjiya daga maharan. Hakan ya haifar da musayar wuta da ta ɗauki tsawon wasu mintuna.

Wani mazaunin yankin, John Dalyop, ya ce bayanan da suke da su sun nuna cewa an kashe jami’an tsaro biyu a arangamar. Ya ce maharan sun kuma kwace bindigogin jami’an da suka kashe kafin su tsere.

An samu raunuka da bacewar mutum

Wani mazaunin yankin, Chollom Jerry, ya ce mutane da dama sun samu raunuka sakamakon harin. Ya kuma bayyana cewa an samu rahoton bacewar wani farar hula bayan faruwar lamarin.

Jerry ya ce harin ya ƙara jefa mazauna Jol da sauran yankunan da ke makwabtaka da ita cikin fargaba da damuwa game da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara yawan jami’an da ke sintiri domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yadda yan bindiga suka rika tashin mutane daga barci, su harbe su har lahira

An tura ƙarin jami’an tsaro

Ƙoƙarin samun martani daga hukumomin tsaro, ciki har da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Plateau, bai yi nasara ba.

Sai dai wasu majiyoyi a hedikwatar ‘yan sanda da ke Jos sun bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da lamarin ya shafa.

Har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, hukumomin tsaro ba su bayyana sunayen jami’an da aka kashe ko cikakken bayani kan yadda harin ya faru ba.

An sha kai hare-hare a Riyom Harin na baya-bayan nan ya ƙara shiga cikin jerin hare-haren da suka shafi fararen hula da jami’an tsaro a Riyom da sauran sassan Jihar Plateau a cikin makonnin baya.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta ce a ranar 4 ga Agusta, an kai hari kan wata tawagar jami’an tsaro ta haɗin gwiwa a hanyar Ganawuri zuwa Sabon Gida a Riyom.

A wannan harin, an kashe wani ɗan sanda da wani Kofur na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya. Maharan sun kuma kwace bindigogin jami’an da aka kashe, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da samame da bincike a wasu al’ummomin da ke kewaye.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

'Yan bindiga sun sace mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindigan sun sace wani likita da matar Hakimi a karamar hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.

Dakarun rundunar Operation 'Enduring Peace' (OPEP) sun kaddamar da aikin ceto da farmaki domin ceto mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng