Kurunkus: Danjuma Goje Ya Raba Gardama kan Batun Ficewa daga APC zuwa Wata Jam'iyya
- Sanata Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta Tsakiya ya bayyana matsayarsa kan ci gaba da zama a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Gombe ya ce kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Goje ya ce shirye-shiryen tallafa wa al’umma da yake yi za su ci gaba ko yana Majalisar Dattawa ko ya bar ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya sake tabbatar da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sanata Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar cewa zai sauya sheƙa zuwa wata jam’iyyar siyasa gabanin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman, Alhaji Ahmed Isa Kashere, ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
Magoya baya sun nemi sanin matsayarsa
Dubban magoya bayan Goje sun taru a gidansa da ke Gombe ranar Asabar domin nuna masa biyayya tare da neman ya bayyana musu matakin siyasar da za su ɗauka gabanin zaɓen 2027.
A yayin ganawar, Goje ya yi alkawarin cewa zai sanar da su matakin da zai ɗauka a fannin siyasa cikin wannan mako.
Wace matsaya Sanata Goje ya cimmawa?
A cikin sanarwar, Sanata Danjuma Goje ya bayyana cewa bai sauya sheƙa daga APC zuwa wata jam’iyya daban ba, rahoton Daily Trust ya nuna hakan.
Goje ya ce kasancewarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC ya sa ba shi da niyyar barin jam’iyyar.
“Ban sauya sheƙa zuwa wata jam’iyyar siyasa ba. A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC, har yanzu ni ɗan jam’iyyar ne."
“Bisa la’akari da shekarun da na yi ina yi wa ƙasa hidima da muƙaman da na riƙe, bai dace a wannan matakin na rayuwata na koma wata jam’iyya kawai domin neman kujerar Sanata ba. Da a ce ina neman wani matsayi mafi girma, da lamarin ya bambanta,” in ji shi.
Ya kuma buƙaci magoya bayansa da ke Gombe da sauran sassan ƙasar su ci gaba da bai wa shugabannin jam’iyyar haɗin kai tare da kasancewa masu biyayya ga APC.
“Wannan gidanmu ne. Mu ne muka gina shi, kuma za mu ci gaba da aiki domin nasararsa,” in ji Goje.
Ya tuna da shekarunsa a siyasa
Da yake waiwayen kusan shekaru 45 da ya shafe yana siyasa, Goje ya ce ya taɓa tsayawa takarar zaɓe sau takwas tun daga Jamhuriyya ta Biyu zuwa yanzu. Ya gode wa Allah bisa samun nasara a dukkan zaɓukan da ya tsaya takara .
Goje ya ce a tsawon shekarunsa a siyasa ya kasance ɗan Majalisar Dokokin Jiha, ya yi wa’adin mulki biyu a matsayin gwamnan Gombe, sannan ya ci zaɓen kujerar Sanata sau biyar. Ya kuma riƙe muƙamin minista tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.
Ya dawo siyasa bayan sanar da ritaya
Goje ya bayyana cewa a shekarar 2019 ya sanar da cewa zai daina neman wani muƙamin siyasa.
Sai dai ya ce magoya bayansa sun matsa masa ya sake tsayawa takarar Majalisar Dattawa a 2023, har suka saya masa fom ɗin takara.
Ya ce sun kuma gaya masa cewa ba lallai ne ya fito ya yi kamfen ba, domin su ne za su yi masa kamfen.
A ƙarshe, Goje ya ce ya samu nasara a zaɓen duk da cewa bai fito ya yi kamfen sosai ba, yana mai nuna godiya ga Allah da magoya bayansa bisa amincewar da suka nuna masa.

Source: Twitter
Shirye-shiryen tallafa wa jama’a za su ci gaba
Sanatan ya kuma tabbatar wa magoya bayansa cewa shirye-shiryen tallafa wa al’umma da yake gudanarwa za su ci gaba ba tare da la’akari da matsayinsa na siyasa ba.
“Ina son tabbatar muku cewa shirye-shiryen tallafa wa jama’ata za su ci gaba ko ina Majalisar Dattawa ko ba na cikinta,” in ji shi.
A halin yanzu, shugabannin jam’iyyun PDP da African Democratic Congress (ADC) na ci gaba da ƙoƙarin shawo kan Goje ya koma cikin jam’iyyunsu gabanin babban zaɓen 2027.
Pantami ya samu goyon baya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan da ya wakilci Gombe ta Arewa, Ambasada Haruna Garba, ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Sanata Haruna Garba ya kuma umarci magoya bayansa da su hada kai da Farfesa Pantami domin cin zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

