'Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Mai Martaba, Sun Bulale Fadawa Sun Tafi da Sarki
- Ƴan bindiga sun kutsa cikin fada, sun sace sarki a karamar hukumar Yagba ta Yamma da ke jihar Kogi a Arewa ta Tsakiya
- Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun lakaɗawa fadawan sarkin duka, kafin su tafi da shi zuwa cikin jeji
- Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma ya yi Allah wadai da harin, yana cewa ba za su bari a ci gaba da cin mutuncin jama'a ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ba sun sace Obalohun na Okoloke, Oba James Dada Ogunyanda, daga fadarsa da ke cikin karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.
An ruwaito cewa maharan sun sace mai martaba Sarkin da sanyin safiya, misalin karfe 2:00 na dare wayewar garin Alhamis, 15 ga watan Mayu, 2025.

Asali: Original
Rahotan Leadership ya nuna cewa harin da ƴan bindigar suka kai fadar basaraken da safe ya haifar da fargaba da tashin hankali a yankin Ƴagba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun koka kan yadda hare-haren masu garkuwa da mutane ke ƙara yawaita a yankinsu.
Yadda 'yan bindiga suka sace sarki
Shaidu sun ce masu garkuwar sun mamaye fadar sarkin da mugayen makamai, inda suka galabaita masu gadi kafin su yi awon gaba da sarkin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Majiyoyin sun ce har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi iyalan sarkin ko masarautarsa domin neman kudin fansa ba, lamarin da ke kara tayar da hankali ga mazauna yankin da ’yan uwansa.
Daga bisani, al’ummar garin sun taru a kusa da fadar suna addu’o’i tare da kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa domin kubutar da sarkin.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Rundunar ’yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa dakaru sun fara bincike da farautar maharan da nufin ceto basaraken.
Ta kuma ƙara da cewa an kafa rundunar hadin gwiwa da ta hada jami’an tsaro da ƴan banga domin farautar masu garkuwar.
Shi ma shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Hon. Tosin Olokun, ya yi Allah wadai da sace sarkin, kamar yadda Punch ta rahoto.

Asali: Getty Images
Ciyaman ya yi tir da dauke sarki
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Adeyemi Sunday, ya fitar, Olokun ya ce yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin na da nasaba da iyakar da suka haɗa da jihar Kwara.
Ya ce:
“Wannan mummunan hari kan babban basarake abin takaici ne da ba za mu lamurta ba, kuma ya sabawa al’adunmu da zaman lafiya. Ba za mu amince da hakan ba.”
Yan bindiga sun sace iyalan hakimi
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun kutsa kai gidan hakimi a jihar Kaduna, sun yi awon gaɓa da matarsa da ɗiyarsa.
An ce maharan sun sace Harira Abdullahi, matar Hakimin Aboro da ke ƙaramar hukumar Sanga a Jihar Kaduna, tare da 'yarsa, Maryam Suleiman Galadima.
Wani mazaunin garin da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Litinin, yana mai cewa al’ummar garin sun shiga firgici
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng