Gwamna Dauda Ya Sake Bayyana Matsayarsa kan Yin Sulhu da 'Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya taɓo batun hawa teburin sulhu da ƴan bindiga masu kai hare-hare
- Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta tattaunawa da ƴan bindiga domin su ajiye makamansu
- Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa ana ladabtar da wasu jami'an Askarawan Zamfara da aka samu da aikata ba daidai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.
Gwamna Dauda ya ce an samu ci gaba a fannin tsaro a jihar, amma har yanzu akwai wasu yankuna da ke buƙatar kulawa ta gaggawa.

Asali: Twitter
Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Tv a ranar Laraba, 14 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce daya daga cikin matakan farko da ya ɗauka bayan hawa mulki shi ne kafa rundunar Askarawan Zamfara, wacce aka horar da mambobinta don taimakawa wajen yaƙi da ƴan bindiga.
Ina aka kwana kan sulhu da ƴan bindiga?
Ya ƙara da cewa jihar Zamfara ba ta yin sulhu da masu laifi, amma waɗanda suka miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba, ana karɓarsu cikin lumana.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bada gudummawar sababin motoci guda 140 ga hukumomin tsaro don ƙarfafa ayyukansu.
“A baya muna jin labarin mutane 200 ko 300 ana kashe su a rana guda. Hare-hare har yanzu suna faruwa, amma sun ragu matuka.”
- Gwamna Dauda Lawal
Batun ba ƴan bindiga haraji a Zamfara
Da aka tambaye shi ko har yanzu wasu ƙauyuka na biyan kuɗin haraji ga ƴan bindiga domin kaucewa hare-hare, gwamnan ya ce hakan na iya faruwa a wasu ƙananan yankuna, amma gaba ɗaya, halin da ake ciki kan tsaro ya inganta.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa yaƙi da rashin tsaro a Arewacin Najeriya dole ne ya kasance na haɗin gwiwa.
Ƙoƙarin gwamnonin Arewa kan yakar rashin tsaro
Ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun gana a Kaduna a ranar Lahadi, kuma za su sake haduwa a Abuja cikin makonni biyu don amincewa kan tsare-tsare na bai ɗaya.
“Idan Zamfara na ɗaukar mataki amma Katsina ko Sokoto ba su yi ba, ƴan bindiga za su koma can."
- Gwamna Dauda Lawal

Asali: Facebook
An ladabtar da wasu jami'an Askarawan Zamfara
Dangane da damuwa kan wuce gona da iri na wasu jami'an rundunar Askarawan Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da cecwa an kori wasu daga cikinsu ko kuma an gurfanar da su a kotu saboda cin amanar aiki.
“Sun fito ne daga cikin ƙauyukan, don haka suna da masaniya kan yankin. Amma ba mu yarda da cin zarafi ko amfani da iko ba bisa ka’ida ba."
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya faɗi abin da gada wajen Matawalle
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana halin da ya tarar da asusun jihar bayan mulkin Bello Matawalle.
Gwamna Dauda ya bayyana cewa abin da ya tarar a asusun jihar Naira miliyan huɗu ne kacal kuma yana da takardun da za su tabbatar da hakan.
Hakazalika ya bayyana cewa rashin samun kuɗi a asusun jihar ya tilasta masa karɓo basussuka domin gudanar da ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng