Gwamnati Ta Gano Yadda ‘Yan Ta’adda Suke Amfani da Sunan Mata Su Samu Kudi
- Hukumar NFIU ta gano yadda kungiyoyi irinsu ISWAP suke samun kudi kuma su kashe ba tare da an gane ba
- 'Yan ta'adda suna amfani da sunayen mata da lambobin wayar mamata wajen bude asusun banki a Najeriya
- An binciko yadda ake aiki da kafofin sadarwa wajen tara tallafin kudi a PayPal ko bankuna daga kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar NFIU ta bankado sabababbin hanyoyin da ‘yan ta’adda suke cigaba da amfani da su domin samun kudin yin barna.
‘Yan ta’adda sun rungumi harkar yin karo-karo daga wajen jama’a a gida da waje domin su samu kudin da suke addabar mutane da su.

Source: Getty Images
'Yan ta'adda na fakewa da sunan mata
Baya ga wannan, jaridar Punch ta rahoto cewa ‘yan ta’addan suna bude asusun banki da sunayen mata domin batar da kama.
Idan aka sa sunayen mata, ba a cika zargin komai ba. Amma maza suke amfani da asusun bankin ta ATM da manhajoji na waya.
Dabarar aiki da lambar wayar matattu a waya
Haka kuma jami’an NFIU sun gano suna amfani da lambar wayoyin mutanen da suka mutu domin cin karensu babu babbaka.
An kuma fahimci cewa da lambobin mamata ko layi masu rajista suke amfani wajen samun sakonni daga wajen bankuna cikin sauki.
Ta hanyar amfani da layin waya da aka yi wa rajista kafin a saida, ba a iya gano su ta hanyar amfani da lambobin fasahar BVN.
Ta haka sai ‘dan ta’adda ya cigaba da aiki da layin waya wato SIM da aka yi wa rajista a kasuwa da sunan wani mutumi can dabam.
Ko an tashi tura sakonni ko kudi kuwa, NFIU ta ce ana amfani da wani salon magana ne da ‘yan ta’addan kadai suke gane juna.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yadda yan bindiga suka rika tashin mutane daga barci, su harbe su har lahira
Za a samu duka wadannan bayanan a rahoton karshen shekara na 2025 da NFIU ta fitar.
Ta ya 'yan ta'adda suke samun kudi?
Rahoton ya ce idan an tashi neman karo-karo, ana amfani da wayoyi sai a fake da neman gudunmuwar taimakon marasa karfi.
An ji cewa ana neman gudumuwar ne ta dandalin sada zumunta na Telagram ko Signal.
Wani lokaci kuma neman taimakon yana zuwa da rigar bunkasa harkar ilmi, a haka ‘yan ta’addan za su bi su sulale da kudi a asirce.
NFIU ta ce da wannan taimako ake lallaban mutane su bada gudumuwar $50 zuwa $500 ta PayPal ko dai wasu bankuna da aka sani.

Source: Getty Images
Idan an tashi dauke kudin da aka tara, ana amfani da asusun bankin ‘yan makaranta da kananan ‘yan kasuwa saboda gudun a ankara.
Da wadannan kudi aka saba sayen abubuwa irinsu keke, taki, babura, na’urorin zamani da sauransu domin yin ta’adi a jihohin Najeriya.
Masu daukar nauyin yan ta'adda
An rahoto Primate Elijah Ayodele ya ce wasu mutane biyar masu karfin iko a Najeriya suna daukar nauyin ta'addanci da garkuwa da mutane.
Ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gano wadannan mutane ta kuma kawar da su domin a samu dorewar zaman lafiya a Najeriya.
Fasto Ayodele ya gargadi gwamnati kan tattaunawa ko sulhu da 'yan ta'adda, ya ce hakan yana mayar da ta'addanci harkar kasuwanci ne kawai.
Asali: Legit.ng

