Karya Ta Kare: An Cafke Rikakken Ɗan Bindiga da Ke Kokarin Tafiya Aikin Hajj a Abuja

Karya Ta Kare: An Cafke Rikakken Ɗan Bindiga da Ke Kokarin Tafiya Aikin Hajj a Abuja

  • uRahotanni sun ce an kama wani da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane a sansanin aikin Hajji da ke Abuja
  • Wanda ake zargin ya dade yana barna inda hukuma ta tabbatar cewa an dade ana nemansa saboda zargin aikata garkuwa da mutane
  • Wani jami’in hukumar jin dadin alhazai ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yayin da DSS suka dauke shi bayan tantance takardunsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Dubun wani hatsabibin mai garkuwa da mutane ta cika bayan da jami'an tsaro suka cafke shi a Abuja.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin ne a sansanin aikin hajji a Abuja yayin tantance maniyyata.

An kama mai garkuwa da mutane a Abuja
An cafke rikakken ɗan bindiga a sansanin alhazai a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

An cafke dan bindiga zai tafi aikin hajji

Daily Trust ta ce jami'an tsaro sun kama Yahaya Zango da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane da karbar kuɗin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiyar tsaro daga sansanin ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin ranar Lahadi 18 ga watan Mayun 2025.

Ya ce an cafke wanda ake zargin ne yayin da ake tantance alhazai da za su tashi zuwa Saudiyya domin aikin Hajji.

Majiyar ta ce wanda ake zargin da aka bayyana sunansa a matsayin Yahaya Zango, dan yankin Paikon-Kore ne a Gwagwalada.

Ya ce jami’an tsaro sun bayyana shi a matsayin wanda ake nema bayan da aka danganta shi da wasu garkuwa da mutane.

Ya kara da ce wanda ake zargin ya gabatar da fasfonsa tare da sauran alhazan Abuja da ke shirin tafiya aikin Hajji bana.

“Da rana ne lokacin tantancewa a sansanin hajji da ke filin jirgin sama jami’an DSS suka cafke shi suka tafi da shi."

- Cewar majiyar

An cafke mai garkuwa da mutane a Abuja
An dan bindiga a sansanin alhazai a Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda dan bindigar ke gudun jami'an tsaro

Wani babban jami’i a hukumar jin dadin alhazai, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kama wanda ake zargin.

Rahotanni sun gano cewa wanda ake zargin yana buya tun da jami’an tsaro suka fara nemansa ruwa a jallo.

Da aka turo mata sakon waya, kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce:

“Kun ce DSS, ni dai Kakakin ‘Yan sandan FCT ce.”

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, hukumar DSS ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

A halin yanzu Najeriya na fama da matsalar yan bindiga mai tsanani, inda kokarin da ake yi bai kai ga nasara sosai ba.

Yan sanda sun kai samame maboyar miyagu

Kun ji cewa ‘yan sandan Abuja ta kama mutane 136 a wani samame da ta kai maboyar ‘yan fashi da sauran miyagu a unguwanni daban-daban a Abuja.

An kai samamen ne da misalin ƙarfe 11:40 na rana inda aka kai farmaki a gine-ginen da ba a kammala ba da wuraren da ake zargi da kasancewa mafakar masu laifi.

Sun kwato makamai da tabar wiwi da wasu miyagun ƙwayoyi daga hannun waɗanda ake zargi, kuma an fara tantance su kafin gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.