Tsautsayi: Ɗan Sanda Ya Ɗirke Ɗalibar da ke Shekarar Karshe a Jami'a, Ta Rasu Nan Take
- Ɗan sanda ya harbe ɗalibar jami'a da ke ajin karshe a shingen binciken ababen hawa a Makurɗi, babban birnin jihar Benue
- Ganau sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ɗalibar ke hanyar komawa makaranta a cikin motar bas ta haya
- Ƙawaye da masu kare haƙƙin ɗan adam sun buƙaci a gaggauta ɗaukar mataki kan wanda ya yi wannan aika-aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a garin Makurdi da wata ɗaliba da ke 400-Level a Jami'ar Kwararafa, Wukari, ta rasa rayuwarta a shingen binciken ababen hawa.
Rahotanni sun nuna cewa harsashin da wani ɗan sanda ya harba ne ya ɗirke ɗalibar mai suna, Ahenjir Emmanuella har lahira a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Asali: Facebook
Lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a, da misalin ƙarfe 8:00 na safe, a shataletalen Wurukum, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'ai daga rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai sun saba tsayawa a shataletalen domin binciken motoci da sauran ababen hawa.
Yadda ɗan sanda ya yi aika-aika
Shaidu sun ce ɗaya daga cikin jami’an ƴan sandan ya saki wuta kan motar da ɗalibar ke ciki ba zato ba tsammani, harsashin ya fasa bas din ya sami Emmanuella
An ce Emmanuella na hanyarta ta komawa makaranta lokacin da wannan mummunan lamari ya afku har ta kai ga rasa rayuwarta.
Igbor Iorbo, wata ƙawarta Emmanuella, ta bayyana cewa:
"Da safiyar yau ne jami’an ƴan sanda suka harbe ƙawata, Emmanuella. Ba ma roƙon komai sai adalci. Ya kamata a gano waɗanda ke da hannu cikin wannan kisa kuma a gudanar da bincike na gaskiya da gaskiya.
An buƙaci a yi wa ɗalibar da aka kashe adalci
Haka zalika, Ukan Kurugh, wani mai rajin kare haƙƙin ɗan adam da walwalar mata, ya nuna matuƙar ɓacin rai bisa yadda rundunar ‘yan sanda ta yi shiru kan wannan lamari.
A ruwayar Punch, Ukah Kurugh ya ce:
"Tun safe lamarin ya faru amma har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yan sanda.
"Idan har ba a bayyana sunan jami’in da ya yi wannan aika-aika ba kafin ƙarshen mako, za mu shirya zanga-zangar lumana mafi girma a Makurdi.”

Asali: Twitter
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Duk ƙoƙarin jin ta bakin CSP Catherine Anene, jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Jihar Benue, ba ta kai ga nasara ba domin ba ta ɗaga kiran wayar salula ba.
‘Yan Najeriya da dama, musamman a shafukan sada zumunta, na ci gaba da nuna fushi da rashin jin daɗi kan yadda jami’an tsaro ke halaka rayukan fararen hula ba tare da hukunta masu laifi ba.
An kama ɗalibar da ta sace kanta a Ekiti
A wani labarin, kun ji cewa asirin wata ɗalibar jami'a ya tonu bayan ta yi karyar cewa an yi garkuwa da ita a jihar Ekiti.
Dalibar ta aika wa 'yar uwarta saƙon ƙarya cewa an yi garkuwa da ita, amma bincike ya nuna ta kwana tare da saurayinta a Ado-Ekiti.
'Yan sandan jihar Ekiti sun samu nasarar cafke dalibar wacce ke ajin ƙarshe a jami'ar jihar Ekiti (EKSU), Helen Kayode.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng