‘Yan bindiga Sun Sace Matar Sarki, Sun Hau da TikTok Sun Nemi a Aiko Masu N20m

‘Yan bindiga Sun Sace Matar Sarki, Sun Hau da TikTok Sun Nemi a Aiko Masu N20m

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Baale na garin Dabu, wato Iya Ayoka, daga fadar ta ranar Juma'a
  • Masu garkuwar suna neman naira miliyan 20 kafin su saki Fasilat Babatunde, wata 'yar shekara 23 a yankin
  • Kungiyar 'Kwara South Development Forum' (KSDF) ta roki gwamnati da jami'an tsaro da su kawo agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kwara - Wasu da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da mai dakin Mai martaba Baale na Dabu a jihar Kwara.

Baale na Dabu, sarki ne a yankin a karamar hukumar Ifelodun, daya daga cikin garuruwan da rashin tsaro ya shafa a Kwara.

Yan bindiga
Wani gari da 'yan ta'adda suka fitine shi a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Yan bindiga sun koma Kudancin Kwara

A karshen makon jiya ne jaridar Premium Times ta kuma rahoto cewa ‘yan bindigan suna neman kudi bayan sun dauke wata mata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, an sace matar hakimi da likita a Kaduna

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya N20m kafin su saki wannan mata da aka dauke ta a wani kauye da yake kusa da nan.

Kungiyar KSDF da aka kafa domin cigaban al’ummar kudancin Kwara ta ce an ce an sace Iya Ayoka ne a Dabu a ranar Juma’a.

Mutanen kudancin jihar Kwara sun dauki lokaci suna fama da matsalar garkuwa a mutane, kashe-kashe da sauran kalubale.

Kungiyar KSDF ta koka kan barnar 'yan bindiga

A wani jawabi da kungiyar KSDF ta fitar, ta yi kira ga gwamntocin tarayya da na Kwara da su gaggauta ganin an fito da Ayoka.

Sakataren kungiyar, Olasehinde Oluwatoba ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar a madadin shugabansa, Obashola Ridwan.

Mista Obashola Ridwan ya nuna ba za su biya sisin kobo domin kubutar da matar ba domin kudin jama'a duk ya kare a biyan fansa.

“Ba mu shirya biyan ko sisi ba. Gwamnati tana bukatar ta dawo mana da ita."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake da wasu mutane

- Obashola Ridwan

Sai an biya N20m kafin a saki Fasilat Babatunde

Jawabin da Oluwatoba ya sa wa hannu ya nuna yadda kungiyar ta ke takaicin cigaba da tsare wata mata Fasilat Babatunde a cikin jeji.

An dauke Fasilat Babatunde mai shekaru 23 a kauyen Wande duk a Ifelodun in ji The Guardian.

Kwanaki kusan 40 da suka gabata aka je har gida aka dauke matar, sannan aka harbi mahaifinta lokacin da ya yi kokarin ya tsere.

Yanzu ‘yan bindigan sun ce idan ba a biya su N20m, ba za su fito da ita ba. Yanzu haka tsohon nata kuma yana jinya kan gadon asibiti.

Wani gari da 'yan ta'adda suka fitine shi
Motar sojojin Najeriya da hoton wani gari bayan harin 'yan ta'adda Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maharan sun yi nasarar shiga shafinta na TikTok, da shi suke amfani wajen wallafa bayanai da yin tuntubar gida a yi zancen kudin fansa.

Baya ga haka, KSDF ta ce mutane suna ta barin gidajensu a kauyen duk da an aiko sojoji zuwa Omu-Aran a karamar hukumar Irepodun.

Kara karanta wannan

'Ku fara kare kanku': Dan majalisar Amurka ya fada wa 'yan Najeriya gaskiya

Mutanen da aka sace sun kubuta

Rahoton nan ya ce mutane 315 da aka sace daga Kebbi, Kwara da Neja sun samu 'yanci bayan shafe watanni shida a hannun 'yan ta'adda.

Yara 25 sun rasu a hannun masu garkuwar kuma tuni aka birne su a daji, yayin da matasa 12 suka shiga cikin 'yan ta'addan da suka fitini jama'a.

Mata biyu da aka sace suna da ciki sun dawo da jariransu, kuma yanzu haka gwamnatin jihar Kwara tana kula da lafiyar wadanda aka sakon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng